Bayan Shekara 3 Ana Farautarsa, Babban Dillalin Kwayoyi a Najeriya Ya Shiga Hannu

Bayan Shekara 3 Ana Farautarsa, Babban Dillalin Kwayoyi a Najeriya Ya Shiga Hannu

  • Hukumar NDLEA ta kama babban dilan miyagun kwayoyi Sunday Ibigide, inda aka kwace kilo 138 na tabar wiwi daga hannunsa
  • A Enugu, jami’an NDLEA tare da sojoji sun lalata gonakin wiwi har kadada 15, sun kwato kilo 37,500 da dubban kwayoyin tramadol
  • Baya ga haka, NDLEA ta kama uwa da ɗanta a Lagos da kilo 149 na wiwi, sannan ta kwato magungunan buguwa na biliyoyin Naira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami’an hukumar NDLEA sun kama fitaccen mai safarar kwayoyi, Sunday Ibigide, a jihar Delta, bayan shekaru uku ana farautarsa.

An kama wanda ake zargin mai shekaru 36 ne yayin da yake ƙoƙarin rarraba sunki 250 na tabar wiwi (skunk) masu nauyin kilo 138.

NDLEA ta kama babban dillalin kwayoyi da ta yi shekaru uku tana farautarsa a Rives
NDLEA ta saki hotunan Sunday Ibigide, babban dilan kwayoyi da ta kama a Rivers. Hoto: @Nationainsight
Source: Twitter

NDLEA ta kama babban dilan kwayoyi

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce Ibigide ya tsere ne a ranar 19 ga Maris, 2022, lokacin da aka alakanta shi da kilo 24.137 na tabar wiwi da gram 10 na molly, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jami'an tsaro sun cafke shugaban PDP da jami'an INEC

Daga ƙarshe, an cafke shi a ranar 10 ga Agusta, 2025, tare da abokin aikinsa Clement Osuya mai shekaru 27.

A wani samame daban, jami’an NDLEA tare da sojoji da 'yan sa kai na ƙauye sun kai samame gonakin wiwi guda uku a Enugu Ezike, jihar Enugu.

Wannan samame ya kai ga lalata wiwi mai nauyin kilo 37,500 da aka shuka a kan kadada 15, tare da kama mutane shida. An kuma kwato kilo 74.5 don gurfanar da su a kotu.

Haka nan a Enugu, jami’an sintiri a ranar 16 ga Agusta sun kama kwayoyi 20,700 na tramadol da cocodamol daga hannun Emmanuel Ayogu mai shekaru 53.

NDLEA ta cafke miyagun kwayoyi masu yawa

Sannan jami'an sun cafke wasu biyu — Nsubechukwu Achidde mai shekaru 24 da Osiaja Frank mai shekaru 41 — da kilo 27.6 na skunk a New Market.

A Lagos, jami’an NDLEA sun kama uwa da ɗanta, Muyibat Mumuni mai shekaru 52 da Faruk Mumuni mai shekaru 25, da katan 298 na tabar wiwi “Ghana Loud” masu nauyin kilo 149 a Mushin a ranar 13 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

Haka kuma, an cafke wani mutum mai suna Emmanuel Samuel a Ajah, Lekki, da kilo 8.5 na tabar wiwin Canadian Loud.

Daga cikin manyan kamen bana, NDLEA a tashar jiragen ruwa ta Onne, jihar Rivers, ta kwato kwalabe 875,000 na maganin codeine (da darajarsu ta haura ₦6.1bn) da kuma kwayoyi miliyan 3.5 na tramadol da benzhexol (da kudinsu ya kai ₦1.7bn) a ranar 13 da 14 ga Agusta.

NDLEA ta kama Sunday, babban mai safarar kwayoyi da ta shafe shekara 3 tana nema
NDLEA ta saki hotunan Sunday Ibigide, babban dilan kwayoyi da ta kama a Rivers. Hoto: @Nationainsight
Source: Twitter

Kamen da NDLEA ta yi a jihohi 7

Wasu manyan samamen sun haɗa da:

Jihar Edo: An kwato kilo 432 na wiwi a hanyar Warake–Auchi da kuma kilo 130 a Sobe, Owan West.

Jihar Kano: An kama Tahiru Manga (25) da Ibrahim Audu (47) da kilo 92 na wiwi a hanyar Zariya–Kano.

Jihar Gombe: An kwace kwayoyi 128,000 na tramadol daga hannun Sani Mohammed (32) a ranar 11 ga Agusta.

Jihar Kogi: An kwato kwayoyi 337,800 na tramadol daga motar haya wadda Sulaiman Oyedokun (47) ke tukawa.

Jihar Taraba: An lalata kilo 11,250 na wiwi a dajin Tanmiya a ranar 12 ga Agusta; an kuma kwace kwayoyi 29,840 na tramadol a Wukari.

Kara karanta wannan

Amurka na shirin sayar wa Najeriya bama bamai masu linzami da wasu makamai

Jihar Kaduna: An kama mutane hudu da kwayoyi 22,640 na tramadol/rohypnol da kuma kilo 111.1 na wiwi.

Lagos–Badagry: An cafke Akeem Adegun da allurai 4,320 na maganin ketamine a ranar 11 ga Agusta.

NDLEA ta cafke masu safarar kwayoyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an hukumar NDLEA sun kai samame kan wuraren da take zargin ana aikata laifuffuka a Kano.

A yayin da ma'aikatan suka kai samame, sun samu nasarar cafke mutanen da ake da aikata laifuffukan da suka shafi harkar miyagun kwayoyi.

Hazalika NDLEA kwato kala daban-daban na miyagun kwayoyi daga hannun mutanen da ake zargi suna safararsu a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com