Majalisa na gab da zartar da doka mai tsauri a kan masu noma, sayarwa da shan tabar wiwi
- Kwanan nan gidan yarin da ke fadin kasar nan za su zama wurin zamar masu noma, sayarwa, da zukar tabar wiwi
- Wani bincike ya nuna cewa kimanin kaso 10.8% na 'yan Nigeria, fiye da mutum miloiyan goma, na amfani da tabar wiwi
- Duk da tu'ammali da tabar wiwi haramun ne a Nigeria, wani bincike ya nuna cewa kasar ta zama cibiyar samun tabar wiwi ga sauran kasashen Afrika ta yamma
Yan majalisar wakilai ta tarayya na dab da samar da wata doka da za ta daure duk mai noma, ko mai sayarwa ko mai shan tabar wiwi a gidan kurkuku na tsawon lokaci, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Tun da fari dai shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa, shine wanda ya gabatar da ƙudurin neman gyara dokar da ake da ita wacce ta haramta ta'ammuli da tabar wiwi.
Idan za'a iya tunawa dai a rahoton majalisar ɗinkin Duniya kan ta'ammuli da ƙwaya na shekarar 2018, ya nuna Najeriya ce ƙasar da ta fi kowacce a duniya zuƙar tabar wiwi.
KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri
Wanda hakan ya nuna cewa sama da yan Najeriya miliyan 10 ne ke ta'ammuli da tabar wiwi.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Doguwa, wanda shine ke wakiltar Tudun-Wada/Doguwa a majalisar wakilai ta tarayya, ya bayyana cewa kudurin zai rage amfani da ganyen da yan Najeriya ke yi.
KARANTA: Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya
Ya ce "Kudirin na kan karatu na biyu kuma ana sa ran zai rage yadda matasan mu ke amfani da ita wannan tabar wiwi." Kamar yadda ya shaidawa jaridar Vanguard.
A baya Legit.ng a rawaito cewa wani mamba a majalisar wakilai ta tarayya na gab da shiga tsaka mai wuya sakamakon kiran da ya yiwa majalisar da ta tsige shugaban ƙasa bisa gazawa wajen samar da tsaro a Najeriya.
Dan majalisar wakilan, Kingsley Chinda, mai wakiltar Obia/Akpor kuma ɗan jam'iyyar PDP, ya bukaci da a tsige shugaba Muhammadu Buhari ranar 7 ga Disamba biyo bayan yankan rago da yan kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma a Zabarmari.
Kazalika, ya ce bai kamata a bar batun kin bayyanar da shugaban kasar ya yi a zauren Majalisar don karin bayani kan taɓarbarewa tsaro ta wuce haka ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng