Zuru: Fitaccen Sarki a Arewacin Najeriya Ya Rasu Yana da Shekaru 81 a Duniya
- Jihar Kebbi ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru da ke jihar a Arewa maso Yamma a Najeriya
- Sarkin Zuru, Janar Muhammad Sani Sami Gomo II, tsohon gwamnan soja na Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya a jiya Asabar a London
- Marigayin ya shiga aikin soja a 1962, ya yi horo a Najeriya da kasashen waje, kafin a nada shi gwamnan Bauchi bayan juyin mulki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zuru, Kebbi - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Sarki Zuru a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya ya rasu.
Sarkin Zuru, Mai Martaba Janar Muhammad Sani Sami Gomo II (rtd), ya rasu yana da shekara 81 a duniya bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Source: Facebook
Kebbi: Yaushe marigayi Sarkin Zuru ya rasu?
Wata majiyar fada ya tabbatar wa Tribune cewa tsohon gwamnan soja na Bauchi ya rasu a jiya Asabar a wani asibiti da ke London.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An haife shi a Zuru, inda ya shiga aiki a rundunar soji a ranar 10 ga Disamba 1962, ya samu horo a gida da waje.
Sarkin Zuru ya zama gwamnan soja na Bauchi bayan juyin mulkin 31 ga Disamba 1983 wanda ya kawo marigayi Janar Muhammadu Buhari kan karagar mulki.
Ya rike mukamin gwamnan Bauchi har zuwa watan Agusta 1985, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya kifar da gwamnatin Janar Buhari ya karbi iko.

Source: Original
Zuru: Sanarwar da gwamnatin Kebbi ta fitar
Rahoton Vanguard ya ce ya samu sanarwar daga Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta na jihar Kebbi, Abubakar Dutsin Mari.
Dutsin Mari ya bayyana cewa marigayi Sarkin Zuru ya rasu a asibitin London bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata har guda huɗu da ’ya’ya bakwai a duniya inda ya yi masa addu'ar samun rahama.
Dutsin Mari ya ce:

Kara karanta wannan
Al Makura: Ƴan bindiga sun bi dare, sun sace hadimin tsohon gwamna, an bazama daji
“Muna bakin cikin sanar da rasuwar Sarkin Zuru, shugaba jarumi mai kishin al’umma.”
Gwamnatin jihar Kebbi ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, masarautar Zuru da daukacin jama’ar Kebbi tare da addu’ar Allah ya ba iyalinsa hakurin jure rashi.
Kwamishinan ya kara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana’iza nan gaba, yayin da gwamnatin Kebbi ke cikin jimami.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wani karin bayani kan shirye-shiryen jana'izar marigayin ko kuma lokacin da za a dawo da shi zuwa gida Najeriya.
Ɗan kasuwa a Arewa ya bar duniya
Kun ji cewa fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim, ya rasu a asibiti a Abuja da safiyar Asabar 16 ga watan Agustan 2025 yana da shekara 88.
Ibrahim ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar NPN ta Jamhuriyar biyu, ya kuma kafa Mighty Jets tare da ɗauko koci daga kasar Brazil.
Dan uwansa, Dr. Musa Ibrahim, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a yi jana’izarsa bayan sallar Azahar a babban Masallacin Abuja da ke Tsakiyar Najeriya.
Asali: Legit.ng
