'Ba Ta da Amfani': Wani Ya Yanke Mazakutarsa kan Rabuwa da Matarsa, ya Shiga Wani Hali

'Ba Ta da Amfani': Wani Ya Yanke Mazakutarsa kan Rabuwa da Matarsa, ya Shiga Wani Hali

  • Wani mutum mai shekara 50 a Bama, Borno, ya yanke al'aurarsa bayan tsohuwar matarsa ta ƙi komawa gidansa duk da roƙonsa
  • Shaidu sun bayyana cewa Modu Isa ya caka wuƙa a cikinsa sau uku, sannan ya sare al'aurarsa, al’umma suka garzaya domin taimaka masa
  • Rundunar ‘yan sanda ta kai shi Asibitin Gwamnati na Bama, aka kwashe shari’ar zuwa CID Maiduguri don ci gaba da bincike kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bama, Borno - Wani mutum a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas ya illata kansa bayan sun samu sabani da matarsa.

Lamarin ya tayar da hankali wanda ya faru a garin Bama da ke Jihar Borno a daren Juma’a 15 ga watan Agustan 2025.

Wani a Borno ya yanke al'aurarsa saboda fushi
Sabon Kwamishinan yan sanda a jihar Borno. Hoto: Nahum Kenneth Daso.
Source: Facebook

Wani ya yanke mazakutarsa a Borno

Kara karanta wannan

Ana zargin sukar gwamnati ta jawo kai hari kan jigon APC, ya sha da ƙyar a Abuja

Rahoton The Nation ya ce mutumin mai shekara 50, Modu Isa, ya yi ƙoƙarin kashe kansa bayan tsohuwar matarsa ta ƙi dawowa gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa lamarin ya faru a unguwar Hausari da misalin yammacin Juma’a da ga gabata.

Wannan ya girgiza mazauna yankin inda wasu ke jimami yayin da wasu ke Allah wadai kan lamarin.

Shaidu sun ce Isa ya caka wa kansa wuƙa sau uku a ciki sannan ya sare al’aurarsa da wuƙa, kafin jama’a su taru suka kira jami’an tsaro.

’Yan sanda sun isa wajen da gaggawa, suka karbe wuƙar a matsayin shaida, sannan suka kwashe shi zuwa Asibitin Gwamnati na Bama domin kula da shi.

Bayan haka, an mika shari’ar ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) a Maiduguri domin gudanar da bincike kan ainihin dalilin wannan mummunan lamari.

An gano cewa tsohuwar matarsa, Bayanxe Modu, wadda ya sake sau uku, ta ƙi amincewa ta koma gidansa, lamarin da ya jefa shi cikin bakin ciki.

Mutane sun kasu da wani ya yanke mazakutarsa a Borno
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Martanin wasu kan lamarin da ya faru

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa mutane da dama sun yi martani kan lamarin kamar yadda ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa

“Ya ce idan Bayanxe ba za ta ci gaba da zama da shi ba, to al'aurarsa ma dole ta tafi,”

- In ji wata makwabciyarsa

Ta ce har yanzu tana kokawa da fahimtar abin da ya faru wanda ya yi matukar ba ta mamaki.

Ma’aikatan asibiti sun yi gaggawar yi masa tiyata suka maido masa da ita a asibiti domin ya ci gaba da rayuwa.

Wata majiyar asibiti ya tabbatar da cewa:

“An dawo masa da mazakuta, kuma tana nan da rai yana ci gaba da karbar magani.”

Wani dattijo a asibitin jinya ya ƙara da cewa:

“Wannan ba yunƙurin kashe kai ba ne, wannan wasan kwaikwayo ne a Borno, Sai a Borno ne mutum zai rasa mazakutarsa a ranar Juma’a kuma a dawo masa da ita a Lahadi.”

An samu gawar miji da mata a Borno

Mun ba ku labarin cewa an shiga tashin hanakli da iyalai hudu suka mutu kwatsam a kauyen Chatta da ke Hawul a jihar Borno, lamarin da ya tayar da hankalin jama'a.

Kara karanta wannan

Jerin manyan kujerun gwamnatin tarayya da Tinubu ya ba mutanen Kano a shekaru 2

An gano gawarsu ne a cikin daki bayan wani dan uwansu ya ziyarci gidan da safe, ya tarar da shiru a gidan kamar ba kowa.

Ana zargin guba ko hayakin janareto ne ya yi sanadin mutuwar; hukumomi sun fara bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.