Saura Turji: Jami'an Tsaro Sun Cafke Shugaban Kungiyar 'Yan Ta'addan Ansaru
- Jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarar cafke shugaban kungiyar ta'addanci ta Ansaru da ke ayyukanta a wasu jihohin Arewacin Najeriya
- Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, shi ne ya sanar da cafke shugaban kungiyar ta Ansaru mai suna Abu Baraa
- Kamun Abu Baraa na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun dade suna nemansa ruwa a jallo domin a cafke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jami’an tsaron Najeriya sun kama shugaban kungiyar ta’addanci ta Ansaru da ake nema ruwa a jallo, Abu Baraa.
Shugaban kungiyar ta Ansaru, Abu Baraa, ana zargin shi ne ya shirya manyan hare-hare da dama a kasar nan.

Source: Facebook
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na musamman da aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban 'yan ta'addan Ansaru ya shiga hannu
Nuhu Ribadu dai yana tare da hafsoshin tsaro gaba ɗaya da kuma manyan shugabannin hukumomin leken asiri, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Ya bayyana cewa tun watan Mayu ake bibiyar Abu Baraa kafin daga bisani aka kama shi a watan Yuli.
"Ina farin cikin sanar da ku cewa mun kammala wani babban aiki mai haɗarin gaske da aka gudanar bisa bayanan leken asiri, wanda ya kai ga cafke babban shugaban kungiyar ta’addancin Jama’atu Ansarul Muslimina fi-Biladis Sudan, wacce aka fi sani da Ansaru, reshen Al-Qaeda a Najeriya."
"An an kafa kungiyar ne a watan Janairu 2012, bayan wata sanarwa a Kano. Kungiyar ta bayyana kanta a matsayin rukunin da ya balle daga Boko Haram, tana ikirarin zama “mafita mai tausayi.”
- Nuhu Ribadu
Sai dai, a cewar Ribadu, kungiyar ta juya manufar ta zuwa kai hare-hare kan jami’an tsaro, fararen hula, da kuma kadarorin gwamnati.

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7
Sojoji sun taba kashe shugaban kungiyar Ansaru
Kama Abu Baraa ya zama babban ci gaba shekaru tara bayan da rundunar sojoji ta kama shugaban kungiyar ta’addanci ta Ansaru, Khalid al-Barnawi, a shekarar 2016.

Source: Facebook
A shekarar 2012 ne gwamnatin Amurka ta lissafa Barnawi a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan Najeriya uku da ta bayyana a matsayin manyan ‘yan ta’adda na duniya da aka fi sanya ido a kansu.
An sanya sunan Barnawi tare da marigayi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, da kuma wanda ya kafa kungiyar Ansaru, Abubakar Adam Kambar.
Bayan mutuwar Abubakar Adam Kambar a wani samamen sojoji a maboyarsa da ke Kano a watan Maris na 2012, al-Barnawi ne ya ɗauki ragamar jagorancin kungiyar Ansaru.
'Yan bindiga sun kai hari a Benue
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja.
Miyagun 'yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Ejema da ke karamar hukumar Ogbadibo, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Harin da 'yan bindigan suka kai ya jawo sanadiyyar hallaka mutane biyu da raunata wani mutum guda daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
