Shugaba Tinubu Ya Amince da Kashe N16.7bn bayan Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Neja

Shugaba Tinubu Ya Amince da Kashe N16.7bn bayan Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Neja

  • A watan Mayun shekarar 2025, an samu mummunar ambaliyar ruwa wadda ta yi sanadiyyar lalacewar gadar Mokwa da ke jihar Neja
  • Shugaban kasa Bola Ahmed ya amince da fitar da biliyoyin kudi don sake gina gadar cikin gaggawa
  • Ministan yada labarai ne ya sanar da hakan, inda ya yabawa Shugaba Tinubu kan amincewa da fitar da kudaden

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da gaggawar sakin Naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da ke jihar Neja.

Amincewar shugaban kasan na zuwa ne bayan ambaliyar ruwa ta rusa gadar a watan Mayun da ya gabata.

Shugaba Tinubu ya amince a gyara gadar Mokwa
Hoton Shugaba Bola Tinubu yana rattaba hannu kan wata takarda Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Ministocin Bola Tinubu na ziyarar aiki

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya sanar da haka a ranar Asabar a Abakaliki, bayan taron da ya yi tare da ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin rage bashin N4trn ga kamfanonin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman ministan na cikin wata sanarwa ne da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar.

Mohammed Idris dai na jagorantar tawagar gwamnatin tarayya a ziyarar kwanaki uku na duba ayyukan raya kasa da shirin tattaunawa da mutanen yankin Kudu maso Gabas.

Tinubu ya amince da gyara gadar Mokwa

A cewar ministan, amincewar fitar da kudin da Shugaba Tinubu ya yi, hujja ce ta yadda gwamnatinsa ke da saurin mayar da martani kan matsalolin gaggawa da suka shafi muhimman abubuwan more rayuwa.

"Muna godiya ga shugaban kasa, haka kuma muna godiya ga ministan ayyuka. Mun tattauna tare, muka gabatar da batun ga shugaban kasa, wanda cikin kyautatawa ya amince da shi."
"Wannan yana da matukar muhimmanci ga jama’a. Kudaden da aka amince da su, su ne N16.7bn don sake gina gadar."

- Mohammed Idris

Sanarwar ta nuna cewa Mohammed Idris ya jaddada muhimmancin gadar wajen haɗa yankuna, tare da yabawa ma’aikatar ayyuka kan martanin da ta yi tun bayan aukuwar iftila’in, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

Ya kuma gode wa David Umahi bisa aika ƙwararru domin tantance barnar da ta auku bayan rushewar gadar.

"Martaninsa ya kasance cikin gaggawa. Wannan ci gaban ya zama abin farin ciki ga gwamnati da jama’ar Jihar Neja."

- Mohammed Idris

Tinubu ya amince da gyara gadar Mokwa
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, a wajen wani taro Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Minista ya yabawa Shugaba Tinubu

A nasa jawabin, ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaba mai tausayi kuma mai lura da bukatun ‘yan ƙasa, wanda ya jajirce wajen magance matsalolin ababen more rayuwa a faɗin kasar nan.

"Shugaban Ƙasa ya amince sake gina gadar da gaggawa kamar yadda na nema. Ya amince saboda tausayi da kulawarsa."

- Dave Umahi

Gwamnatin Tinubu za ta gyara gadar Mainland

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya aikin gyara ginin gadar Third Mainland da ke birnin Legas.

Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin ta amince da aikin gyaran gadar ne a kan tsabar kudi har Naira tiriliyan 3.6.

Dave Umahi ya bayyana cewa an amince da gyaran gadar ne bayan bincike ya nuna cewa barin ta a halin da take yanzu babban hadari ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng