Zaben Cike Gurbi: Jami'an Tsaro Sun Cafke Shugaban PDP da Jami'an INEC

Zaben Cike Gurbi: Jami'an Tsaro Sun Cafke Shugaban PDP da Jami'an INEC

  • Jami'an tsaro sun kai samame a wan. Otal inda suka cafke shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ogun, Abayomi Tella
  • An dai cafke shi ne tare da jami'an jam'iyyar da kuma wasu jami'ai na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)
  • Jam'iyyar ta fito ta yi martani mai zafi kan kamun, inda ta yi zargin cewa ana kokarin kullawa shugabanta sharri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ogun - Jami’an tsaro sun kama shugaban PDP na jihar Ogun, Abayomi Tella, tare da wasu jami’an jam’iyyar da kuma jami’ai biyu na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Jami'an tsaron sun cafke su ne a wani otal da ba a bayyana sunansa ba da ke yankin Iperu-Remo a jihar Ogun.

Jami'an tsaro sun kama shugaban PDP a Ogun
Taswirar jihar Ogun, Najeriya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an samu mutanen ne dauke da tarin kuɗi a hannunsu.

Kara karanta wannan

APC ta tsorata, ta bukaci INEC ta soke duka zaben cike gurbi a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban PDP da jami'an INEC sun shiga hannu

'Yan siyasar da jami’an INEC ɗin, waɗanda aka nuna ana yi musu tambayoyi a cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta ranar Asabar, an cafke su ne a wani otal da ke Iperu-Remo, ƙaramar hukumar Ikenne, jihar Ogun.

A cikin bidiyon da ya bazu, an ga jami’an INEC namiji da mace, tare da jami’an PDP suna tsugunne wani jami'in tsaro yana yi musu tambayoyi.

A cewar mai tambayar, rahoton leken asiri ya nuna cewa jami’an INEC ɗin sun karɓi tarin kuɗi daga hannun jami’an jam’iyyar PDP don sayen ƙuri’u a yayin zaɓen cike gurbi.

Ya bayyana cewa cafke jami’an hukumar zaɓen ne ya haifar da kama jami’an PDP a otal ɗin da ke Iperu-Remo.

Jami’in INEC ɗin namiji ya shaida wa mai tambayar cewa na gaba da shi ne ya umarce shi da ya je ya karɓi kuɗin daga hannun ‘yan siyasar.

Kara karanta wannan

Zaɓen cike gurbi: Yadda 'yan sandan Kano su ka kama 'yan daba sama da 100

Jam'iyyar PDP ta yi martani mai zafi

Sai dai jam’iyyar PDP ta bayyana cafke Abayomi Tella a matsayin dabarar tsoratarwa da kuma ƙoƙarin hana mambobinta kada ƙuri’a a zaɓen cike gurbi.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Asiwaju Akinloye Bankole, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Ya ce ce jami’an tsaro sun kama Abayomi Tella ne da misalin ƙarfe 3:30 na dare, inda suka balle ɗakin otal ɗinsa.

An cafke jami'an hukumar INEC a jihar Ogun
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, a wajen wani taro Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Ya ce shugaban na PDP yana cikin ɗakin otal ɗinsa yana hutawa tare da direbansa da wani mai taimaka masa lokacin da aka yi awon gaba da shi.

Bankole ya jaddada cewa akasin rahotannin da ake yadawa, babu wani kayan zaɓe da aka samu a hannun Tella, haka kuma ba a kama shi da tarin kuɗi ba.

"Shugaban yana da N100,000 kacal a ɗakinsa. Ba a samu wani kayan zaɓe a ɗakin otal ɗinsa ko a motarsa ba."

Kara karanta wannan

An gano masu kudin da jami'an tsaro suka kama a hannun wakilin PDP a Kaduna

- Asiwaju Akinloye Bankole

PDP ta yi magana kan cafke wakilinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi magana kan zargin cafke wakilinta da kudin sayen kuri'u a Kaduna.

Jam'iyyar hamayyar ta bayyana cewa kudin da aka samu a hannun Shehu Aliyu Pantagi, ba na sayen kuri'un jama'a ba ne.

PDP ta bayyana cewa an ware dukiyar ne don biyan alawus din wakilan jam'iyyar tare da gudanar da zaben cike gurbi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel