Fitaccen Dan Kasuwa a Arewa kuma na Kusa da Marigayi Shehu Shagari Ya Rasu

Fitaccen Dan Kasuwa a Arewa kuma na Kusa da Marigayi Shehu Shagari Ya Rasu

  • Fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim, ya rasu a asibiti a Abuja da safiyar Asabar yana da shekara 88
  • Ibrahim ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar NPN ta Jamhuriyar biyu, ya kuma kafa Mighty Jets tare da ɗauko koci daga Brazil
  • Dan uwansa, Dr. Musa Ibrahim, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a yi jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Najeriya ta yi rashin babban dan kasuwa a Arewacin Najeriya bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.

Marigayi Alhaji Isiaku Ibrahim, babban ɗan kasuwa kuma dattijo daga Arewa, ya rasu a wani asibitin Abuja da safiyar Asabar 16 ga watan Agustan 2025.

Dan kasuwa a Area ya riga mu gidan gaskiya
Marigayi Alhaji Isiaku Ibrahim ya kafa tarihi a Najeriya kafin rasuwarsa. Hoto: Isah Nuhu.
Source: Twitter

'Dan kasuwa a Arewa ya bar duniya

Kara karanta wannan

Ana zargin sukar gwamnati ta jawo kai hari kan jigon APC, ya sha da ƙyar a Abuja

Daily Trust ta ce marigayin wanda ya kasance aboki kuma na kusa ga tsohon shugaban ƙasa, Shehu Usman Shagari ya rasu yana da shekara 88.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin dan kasuwar ya fito daga garin Mangar, a Farin Ruwa na karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa.

An bayyana shi a matsayin ɗan siyasa gogagge wanda ya taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar NPN a Jamhuriya ta biyu.

Baya ga siyasa, Ibrahim ya shahara a harkokin wasanni, a shekarun 1970s, ya kafa kungiyar kwallon kafa ta Mighty Jets Jos.

Shi ne ɗan Najeriya na farko da ya ɗauko koci daga Brazil domin horar da kungiyar.

Marigayin ya kashe miliyoyin Naira wajen tallafa wa kungiyar, inda ya saya musu sabuwar babbar bas ta alfarma, tare da ɗaukar nauyin wasanni a lokacin.

Kungiyar Mighty Jets ta zama abin tsoro ga abokan hamayya a wancan lokaci.

Haka kuma, Ibrahim ya kasance cikin ‘yan Najeriya biyu da suka fara mallakar jirgin sama abin da ya nuna irin bunkasar kasuwancinsa.

Arewa ta yi rashin fitaccen dan kasuwa
Taswirar jihar Nasarawa da kae Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Dan uwan marigayin ya tuna alherinsa

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

'Dan uwansa, Dr. Musa Ibrahim, tsohon babban sakatare a ma’aikatar gwamnati, ya tabbatar da rasuwar.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kaunar mutane, nagarta da kishin yankin Arewa.

Dr. Musa ya ce:

“Cika miƙa lamura ga ikon Allah, muna sanar da rasuwar babban ɗan siyasa da mai bada tallafi, za a yi jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Abuja.”

Ya ƙara da cewa marigayin na daga cikin ‘yan siyasan Arewa na gaskiya waɗanda suka tsaya kan ci gaban yankin da taimakon al'umma.

Dr. Musa ya roƙi Allah ya gafarta masa tare da ba shi Aljanna firdausi da kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.

Babban 'dan kasuwa, Dantata ya rasu

Kun ji cewa shahararren ɗan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 94 a duniya.

Ɗantata ya rasu ne a birnin Abu Dhabi da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa, Sanusi Dantata.

Daga bisani, an yi jana'izar marigayin a Madinah inda manyan yan siyasa da sarakuna a Najeriya suka samu damar halartar sallar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.