'Yan Bindiga Sun Sake kai Hari a Benue, an Hallaka Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Sake kai Hari a Benue, an Hallaka Bayin Allah

  • An samu asarar rayuka a jihar Benue bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani kauye
  • 'Yan bindigan sun kai harin ne a wani kauye dake karamar hukumar Ogbadibo inda suka bude wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Mummunan harin da 'yan bindigan suka kai ya jawo asarar rayuka da raunata wani matashi wanda hakan ya tilasta aka garzaya da shi zuwa asibiti don ba shi kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - ‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum guda a jihar Benue.

Lamarin ya auku ne a wani hari da 'yan bindigan suka kai a kauyen Ejema da ke cikin karamar hukumar Ogbadibo.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Benue
Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, a wajen ganawa da manema labarai Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Benue

Bayanan da aka samu sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 1:55 na tsakar dare, ranar 15 ga watan Agusta, lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba suka mamaye kauyen Ejema.

An bayyana mutanen suka rasa rayukansu da Anthonia Okwori, mai shekaru 55 da haihuwa, da kuma wani saurayi mai suna Gabriel Shaibu, mai shekaru 22, waɗanda aka harbe su har lahira.

Haka kuma wani matashi mai suna Friday Shaibu, mai shekaru 20, ya samu raunukan harbin bindiga.

An garzaya da shi asibitin Divine Care Hospital da ke Orokam, inda yake samun kulawa tare da murmurewa a halin yanzu.

'Yan sandan Benue sun kai dauki

Majiyoyi sun ce bayan aukuwar harin, jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO na Orokam, tare da haɗin gwiwar wata tawagar tsaro, sun shiga aikin sintiri da kai dauki a yankin.

Kara karanta wannan

Katsina: Basaraken da ake zargi da yi wa 'yan ta'adda jagora ya fada komar jami'an tsaro

An dauki matakan tabbatar da tsaro domin hana sake aukuwar makamancin wannan hari.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa an dauki hotunan gawarwakin waɗanda aka kashe, sannan aka kwashe su zuwa babban asibitin Ijadoga domin adanawa a ma’ajiyar gawa da kuma gudanar da binciken likitanci.

'Yan.bindiga sun kashe mutane a Zamfara
Hoton jami'an 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Hakazalika ana ci gaba bincike da kokarin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki domin a gurfanar da su a gaban doka.

Jami’an tsaro sun jaddada aniyar gwamnati wajen tabbatar da cewa babu wanda zai kauce wa hukunci bayan aikata irin wannan laifi.

An kuma bukaci jama’ar yankin da su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’an tsaro goyon baya, ta hanyar bayar da ingantattun bayanai cikin gaggawa domin dakile sake faruwar irin wannan tashin hankali a nan gaba.

'Yan bindiga sun sace hadimin tsohon gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da hadimin tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

'Yan bindigan sun dauke Alhaji Adamu ne a ranar Juma'a, 15 ga watan Agustan 2025 a birnin Lafia.

Miyagun dai sun kutsa cikin gidan hadimin tsohon gwamnan ne sannan suka yi awon gaba da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng