Wani Abin Fashewa da Ake Zargin 'Bam' ne Ya Tashi a Barikin Sojojin Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da fashewar wani abu da ake kyautata zaton bam ne a barikin Ilese da ke jihar Ogun
- Lamarin ya faru ne a daya daga cikin dakunan da sojoji ke ajiyar kayayyaki a safiyar ranar Alhamis, 14 ga watan Agusta, 2025
- Mai magana da yawun rundunar soji ta bayyana cewa abin da ya faru bai yi muni ba domin babu wanda ya rasa ransa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Wani abin fashewa da ake zaton bam ne ya tashi a dakin ajiyar kayayyaki da ke barikin sojoji na Ilese a garin Ijebu-Ode na jihar Ogun.
Fashewar ta faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 14 ga Agusta, 2025, kuma jim kadan bayan hakan, wuta ta kama a wurin.

Asali: Twitter
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele, ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar, rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin sojojin ta bayyana cewa fashewar da ta faru a barikin Ilese a matsayin "karami," tana mai cewa babu wani abin damuwa.
Abin fashewa ya tashi a barikin sojoji
Laftanal Kanal Anele ta ce babu wanda ya rasa ransa a cikin lamarin, ko da yake ginin wurin ya ruguje sakamakon fashewar abin da ake zaton bam ne.
"Da sanyin safiyar yau (jiya Alhamis) 14 ga watan Agusta, 2025, wani abin fashewa ya tashi a daya daga cikin gine-ginen ajiyar kyayyaki na rundunar kwance bam ta 42, wanda ya haddasa tashin wuta kadan.
"Gaggawar da jami'an sojoji suka yi wajen kai dauki tare da taimakon jami'an kashe gobara ta Ijebu-Ode ya sa aka yi nasarar kashe wutar da ta tashi cikin kankanin lokaci.
- In ji Laftanar Kanal Anele.
An sami asarar rayuka a barikin Ilese?
Kakakin rundunar sojojin ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamkon wannan abu da ya faru a barikin sojojin.

Kara karanta wannan
"PDP ba ta rabu ba," Sanata Abba Moro na neman rikita lissafin gwamnoni 2 a Najeriya
“Abu mafi muhimmanci, babu asarar rayuka kuma babu wanda ya ji rauni. Matsalar ta tsaya ne kawai a kan ginin da abin ya shafa da kuma wasu kayayyakin da aka adana a ciki.
"A halin yanzu ana gudanar da cikakken bincike don tantance girman asarar kayan,” in ji sanarwar.

Asali: Twitter
Sojoji sun nemi jama'a su kwantar da hankula
Rundunar sojoji ta bukaci mazauna Ilese da sauran unguwanni makwabta da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum inji rahoton The Cable.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Rundunar sojojin Najeriya, tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa, sun fara cikakken bincike don gano dalilin faruwar lamarin da kuma yadda za a kauce wa maimaituwarsa.”
Sojoji sun kashe yan bindiga sama da 60
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin sama ta yi nasarar hallaka yan bindiga da dama a wani samame da suka kai a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa
Rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya sun gano gawarwakin yan bindiga fiye da 60 a Zamfara bayan luguden wutar da suka yi ta sama.
An kai harin ne kan taron ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton za su kai farmaki a Nasarawan Burkullu na karamar hukumar Bukuyum a jihar Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng