"Ba Gudu, ba Ja da Baya," Naja'atu Ta Karfafa Gwiwar Tambuwal bayan Kamen EFCC

"Ba Gudu, ba Ja da Baya," Naja'atu Ta Karfafa Gwiwar Tambuwal bayan Kamen EFCC

  • Fitacciyar 'yar gwagwarmaya, Naja'atu Muhammad ta ziyarci tsohon gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal bayan EFCC ta sake shi
  • Hajiya Naja'atu ta ce ita da wasu manyan 'yan siyasa sun kai masa ziyarar ne domin ƙarfafa masa gwiwa da jajanta masa kan abin da ya faru
  • Ta bayyana cewa wannan kamu ba zai hana su ci gaba da gwagwarmayar ceto Najeriya daga wadanda ta bayyana a matsayin azzaluman shugabanni ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Fitacciyar ‘yar siyasa kuma ‘yar gwagwarmaya a Arewacin Najeriya, Naja’atu Bala Muhammad, ta kai ziyara ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Ziyarar ta zo ne kwanaki bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama Tambuwal bisa zargin cire kuɗi daga asusun gwamnati ba bisa ka’ida ba a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal
Hoton tsohon gwamnan jihar Sakkwato yayin wata gana wa da 'yan jarida Hoto: Aminu Waziru Tambuwal
Source: Facebook

A wani bidiyo da Naja’atu ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin ƙarfafa masa gwiwa da kuma tabbatar da cewa bai ja da baya daga gwagwarmayar ceto Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina yi maka murna” – Naja’atu ga Tambuwal

A cikin sakon nata, Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa ziyarar ta haɗa da jajantawa da taya murna bayan EFCC ta kama AminuWaziri Tambuwal.

Ta ce:

“Ina yi maka murna, ina yi maka jaje, Allah ka da ya sa ka sare saboda kada mu ji kunya. Ba gudu, ba ja da baya. Allah Ya kare, Allah Ya ba mu nasara.”

Ta kuma yi fatan cewa kamen da EFCC ta yi wa Tambuwal zai zama wata dama ta ceto Najeriya daga “zaluncin” da ake fuskanta a mulkin kasar nan a yanzu.

“Gwamnatin nan dakikiya ce” – Naja’atu

A cewar Naja’atu, gwamnatin Najeriya a yanzu “dakikiya ce” wadda ke jawo wa ƙasar matsaloli masu yawa, tare da shugabanni da ta kira “azzalumai” da ke jagorantar al’amuran ƙasar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan kujerun gwamnatin tarayya da Tinubu ya ba mutanen Kano a shekaru 2

Ta ce:

"Na haɗu da sauran masu yi masa fatan alheri da manyan jami’an siyasa a gidansa Sanata Aminu Waziri Tambuwal bayan sakin sa daga tsarewar da EFCC ta yi ba bisa ka’ida ba.
Aminu Waziri Tambuwal
Tambuwal yayin wani taro a Sakkwato Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Office
Source: Facebook

Hajiya Naja’atu ta kara nanata cewa wannan kame da aka yi masa ba zai dakile masu gwagwarmaya wajen ci gaba da fafutukar ceto Najeriya ba.

A cewarta, abin da ya fi muhimmanci a wannan lokaci shi ne tsayawa kan gaskiya da adalci, tare da kare dimokuraɗiyya daga duk wani yunkurin tauye ta.

Ta jaddada cewa za su ci gaba da haɗa kai da duk wanda yake da gaskiya da tsayin daka wajen kare muradun jama’a.

Tambuwal ya shiga hannun hukumar EFCC

A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, kan zargin cire kuɗi ba bisa ka'ida ba.

Cire kudi ba bisa ka'ida ba abu ne da ya saba wa dokar yaki da safarar kuɗin haram na hukumar EFCC ta shekarar 2022 a kokarin yaki da yi wa kasa ta'annati.

An bayyana cewa Tambuwal ya isa ofishin EFCC da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Litinin, inda ya gurfana gaban jami’an hukumar don amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng

iiq_pixel