Ta Fasu: An Ji Abin da Aminu Tambuwal Ya Fadawa EFCC bayan Ta Kama Shi a Abuja

Ta Fasu: An Ji Abin da Aminu Tambuwal Ya Fadawa EFCC bayan Ta Kama Shi a Abuja

  • Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsa da jami'an EFCC bayan ya amsa gayytar da suka masa
  • A ranar Litinin da ta gabata ne EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Sakkwato a ofishinta da ke Abuja kuma ba ta sake shi ba sai ranar Talata
  • Da yake jawabi bayan ya koma Sakkwato, Tambuwal ya ce matakin da EFCC ta dauka a kansa a yanzu ba komai ba ne illa bita da kullin siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanata mai ci, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi bayani kan tsare shi da hukumar yaki da rashawa (EFCC) ta yi.

Sanata Tambuwal ya bayyana cewa tun farko hukumar EFCC ta gayyace shi, kuma ya amsa tare da mika kansa a ofishinta ranar 6 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa

Tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal
Hoton tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal a ofis Hoto: @AWTambuwal
Source: Twitter

Sau 2 Tambuwal ya kai kansa ofishin EFCC

Ya ce bayan jerin tambayoyi na farko, an bar shi ya koma gida amma aka umarce shi da ya dawo a ranar 10 da 11 ga watan Agusta, 2025 domin karin bincike, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya koma jiharsa watau Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Da yake bada labarin abin da ya faru bayan ya koma wurin EFCC a karo na biyu, Tambuwal ya ce ya amsa tambayoyi na tsawon awanni amma bisa mamaki aka hana ahi tafiya gida.

Me ya faru da Tambuwal a ofishin EFCC

A cewarsa, da ya nemi a bar shi ya koma gida, jami’an EFCC sun dage cewa dole sai ya kawo mutane biyu da za su tsaya masa, musamman daraktoci a Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya kafin a sake ahi.

Tambuwal ya ce:

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta saki tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal

“Na ce musu su koma su gaya wa shugaban EFCC cewa ni tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ne da ba ni da tabo, tsohon gwamna na wa’adi biyu a Jihar Sakkwato, sanata mai ci, kuma mai rike da lambar girmamawa ta CON, ya kamata a bar ni in tafi bisa sanin kaina.

Dalilin da ya sa Tambuwal ya kwana a EFCC

Ya ce duk da rokon da lauyoyinsa suka yi, ciki har da manya masu matsayin SAN uku, jami’an EFCC suka kekashe kasa suka ki sauya sharuddan belin.

"Saboda haka aka tsare ni na kwana a can, washegari kuma bayan cika sharuddan belin sai aka bari na dawo gida," in ji shi.

Sanata Tambuwal ya kalubalanci EFCC kan daukar wannan mataki a yanzu, yana mai danganta shi da wani makirci na siyasa, rahoton Vanguard.

“Me ya sa yanzu?” in ji shi, yana mai nuna cewa gwamnatin Sakkwato ta kafa wani abin da ya kira “kwamitin bincike na bogi” domin binciken mulkinsa, wanda a ganinsa bita da kullin siyasa ne.

Jami'an hukumar EFCC.
Hoton jami'an hukumar EFCC a bakin aiki Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Aminu Tambuwal ya soki gwamnatin Tinubu

Ya ce wadannan abubuwa suna daga cikin kokarin bata masa suna da kuma rufe bakin masu fadawa gwamnatin tarayya a karkashin Shugaba Bola Tinubu gaakiya.

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

"Yanzu dai layi biyu ya rage a Najeriya, wadanda suke tare da Bola Tinubu da gwamnatinsa, da kuma wadanda suke tare da jama’ar Najeriya. Mun zabi tsayawa tare da jama’a,” in ji shi.

Tsare Tambuwal ya fusata Atiku Abubakar

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da matakin EFCC na tsare Aminu Waziri Tambuwal.

Atiku ya yi zargin cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne saboda yana daya daga cikin manyan hadakar yan adawa watau ADC.

A cewar jagoran 'yan adawar Najeriya, abin takaici ne yadda hukumar EFCC ta sauka daga turbar da aka dora ta da kuma tubalin da aka gina ta a kai tun farko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262