'Akwai Sharadi,' Gwamnati Za Ta Fara ba Ma'aikatan Manyan Makarantu Bashin N10m
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da asusun TISSF domin ba malamai da ma’aikatan manyan makarantu rancen kuɗi marar ruwa
- Gwamnati ta ce ma'aikatan za su iya amfani da kudin don kula da lafiya, biyan kudin haya, noma, kasuwanci da sauran bukatun rayuwa
- Ma’aikatan manyan makarantu da suke da sauran shekaru biyar kafin ritaya ne za su iya neman bashin da ya kai Naira miliyan 10
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da asusun tallafawa ma'aikatan manyan makarantu (TISSF) da zai rika ba ma'aikatan rancen kudi marar ruwa.
An kaddamar da asusun TISSF ne domin bunkasa walwalar ma'aikata da kuma kara masu kwarin gwiwa wajen ci gaba da yi wa ilimi hidima.

Source: Twitter
Gwamnati ta kaddamar da asusun TISSF
Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya kaddamar da wannan asusu a wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta ruwa.

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Tunji Alausa ya bayyana wannan asusu a matsayin wata kafa ta ba malamai da ma'aikatan manyan makarantu rancen kudin da suke bukata don gudanar da rayuwarsu cikin mutunci.
Ministan ya bayyana cewa asusun TISSF na karkashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu da zummar daga darajar bangaren ilimi.
Ya ce an samar da asusun domin gina al'umma domin su ne babban jarin kasa wajen sauya fasalin ilimi da kuma ci gaban tattalin arziki.
A cewar ministan, ma'aikatar ilimi ta tarayya da kuma asusun TETFund ne suka samar da shirin tallafin tare da hadin gwiwar Bankin Masana'antu (BoI).
Amfanin ba da rance ga ma'aikatan makarantu
Punch ta rahoto cewa a karkashin wannan shirin, gwamnati ta bayyana wasu dalilai da take fatan malamai da ma'aikatan manyan makarantu za su nemi rancen kudin.
"Malamai da ma'aikatan manyan makarantu za su iya neman rancen kudin domin biyan kudin magani ko kula da kiwon lafiyarsu da ta iyalansu, da kuma biyan kudin haya.

Kara karanta wannan
Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa
"Hakazalika, za su iya yin amfanin da kudin don harkokin zirga-zirga (da ya hada da sayen motocin lantarki ko sauya motocinsu na fetur zuwa na CNG).
"Hakakuma, masu neman bashin za su iya amfani da kudin don fara kasuwanci ko noma, da kuma fadada iliminsu ta hanyar ci gaba da karatu ko halartar shirye-shirye.
- Ministan ilimi, Tunji Alausa.

Source: Twitter
Ma'aikatan makarantu za su samu lamunin N10m
Ministan ya kuma bayyana cewa shirin ya shafi dukkanin ma'aikatan jami'o'in tarayya, kwalejojin fasaha da na ilimi da tarayya da ma wasu manyan makarantun jihohi.
Ya kuma ce dole ne wadanda za su nemi rance su kasance suna da sauran akalla shekaru biyar kafin ritaya, kuma su zama mambobi a kungiyoyi irinsu ASUU, NASU, COEASU, da SSANIP.
"Wadanda suka cancanta za su iya neman rancen kud da suka kai N10m, amma za a kayyade hakan ga kashi 33.3 na albashinsa.
"Za a biya bashin kudin ne a tsawon shekaru biyar, kuma za a fara cire kudin bayan watanni 12 da karbarsu, ba tare da an cire kudin ruwa na ko sisin kwabo ba."
- Ministan ilimi, Tunji Alausa.
Za a dauki ma'aikata a manyan makarantu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya za ta ɗauki sabbabin ma'aikata a manyan makarantu domin cike gurabe da giɓin da ake da su.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya umarci makarantun da aka ba izinin ɗaukar ma’aikata su sanar da guraben aikin da suke nema ta hanyar talla ga jama'a.
Ana ganin wannan umarni na ministan ilimin yana da nufin tabbatar da an bi tsarin ɗaukar aiki na gaskiya, ba da dama ga kowa, da kuma yin adalci yayin tantancewa.
Asali: Legit.ng
