Gwamnatin Tinubu Ta Bude Sabon Shiri, Za a Hada Matasa da Masu Daukar Aiki a Duniya
- Gwamnatin tarayya ta bullo da wani sabon shiri da zai horar da matasa kuma ya bude masu kofofin samun ayyuka a duniya da damarmakin kasuwanci
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya sanar da haka bayan ya karbi jagorancin kamfanin GenU da aka farfado da shi
- Ya ce ana sa ran wannan shirin zai horar da matasa miliyan 20 daga nan zuwa 2030 kuma za a ware wa mata kaso 60% daga ciki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani gagarumin shirin domin haɗa matasa ‘yan Najeriya miliyan 20 da ayyukan yi, horo, da damar yin kasuwanci kafin 2030.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya sanar da hakan yayin da ya karɓi ragamar shugabancin Kwamitin Gudanarwa na kamfanin Generation Unlimited (GenU) na Nigeria da aka farfado da shi.

Source: Twitter
A wata sanarwa da Shettima ya wallafa a shafinsa na X, ya ce wannan shirin zai ware wa mata kaso 60% na wadanda za su amfana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda shirin zai samar wa matasa damarmaki
Shettima ya ce:
"Sama da kaso 60% na al'ummar kasar nan matasa ne yan kasa da shekaru 25, ba zamu yi watsi da su ba domin arziki ne mai girma, ba zamu bari matasan mu su lalace ba.
"Ya zama dole mu inganta matasa, mu zuba jari a cikinsu, sannan mu bude masu damarmakin da za su dogara da kansu ta hanyar kirkire-kirkire da samar da ayyuka."
Mataimakin shugaban kasar bayyana matasan a matsayin “ƙarfin da Najeriya ke da shi na musamman."
Kalubalen da ake fuskanta wajen taimakon matasa
Shettima ya yi gargadin cewa tsarin koyar da matasa su samu gogewa a bangarori daban-daban na zamani yana fuskantar “ƙalubale uku da ya kamata a magance.

Kara karanta wannan
Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu
Ya jero kalubalen da suka hada da rashin hada matasan da damarmaki, rashin samun abin dogaro, da kuma ƙarancin kayan aiki don ba su horo na zahiri mai fadi.
"Shirin ba matasa horo kadai ba zai fitar da mu daga halin da muke ciki ba, muna bukatar mu canza tsarin yadda ake horar da matasa, mu kawo tsari mai nagarta da zai dore."

Source: Twitter
A tsarin za a koyar da fasahar zamani a karkashin shirin Digital Access and Livelihoods Initiative (DALI), wanda zai ba matasa damar haduwa da wadanda za su dauke su aiki ko su samu damar yin kasuwanci.
Shettima ya ce shirin zai kasance karkashin National Skills Qualification Framework domin tabbatar da cewa matasan Najeriya suna da takardun shaida da za su iya yin gogayya a duniya.
Kasashen duniya za su dauki 'yan Najeriya aiki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta hada kai da Saudiyya, Birtaniya, Amurka, Australia, da wasu ƙasashe domin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.
Dingyadi ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da wata ƙasa, yayin da tattaunawa da sauran ƙasashen ta kai matakin karshe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
