Lokaci Ya Yi: Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na Kasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi yayin da tsohon sakatarenta na kasa, Rex Onyeabo ya rasu yana da shekaru 80 a duniya
- Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da suka fitar ranar Alhamis a Enugu, tare da rokon yan Najeriya su sanya shi a addu'a
- Marigayin yana daya daga cikin kusoshin da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998 kuma har zuwa rasuwarsa, yana cikin mambobin BoT
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Tsohon Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sir Rex Onyeabo, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 80 da haihuwa.
Dansa, Dr. Obiora Onyeabo, ne ya bayyana rasuwar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 14 ga watan Agusta, 2025 a jihar Enugu.

Asali: Twitter
A cewarsa, tsohon jigon na PDP ya rasu cikin lumana a ranar 7 ga Agusta, 2025, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"PDP ba ta rabu ba," Sanata Abba Moro na neman rikita lissafin gwamnoni 2 a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sakataren jam'iyyar PDP ya rasu
Sanarwar ta ce:
“Da zuciya mai nauyi amma cikin godiya ga Allah saboda rayuwa mai albarka, iyalan Onyeabo na sanar da rasuwar uba kuma dattijo mai kishin kasa, Cif (Sir) Rex Chuma Onyeabo (KSM)."
"Kafin rasuwarsa, yana rike da sarauta daban-daban da ta hada da Eze-Ugo 1 na al’ummar Igbo a Abuja, Onwa na-etili Ora 1 na Ugbawka, Ijele 1 na Akaegbe-Ugwu da Ada-Idaha na masarautar Efik.
“Cif Rex Onyeabo ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa PDP, ya rike mukamin sakataren jam’iyyar na kasa a 1999, sannan daga baya ya zama mamba a Majalisar Amintattu har zuwa rasuwarsa.
Iyalan marigayin sun kara da cewa za a sanar da tsare-tsaren jana'izarsa nan ba da jimawa ba, inda suka kara da rokon a sanya shi a addu'a.
Takaitaccen bayani kan marigayi Rex Onyeabo
Marigayi Onyeabo ya yi karatun injiniyanci a jami’ar Carnegie Mellon ta Amurka, sannan bayan dawowarsa Najeriya ya sadaukar da kansa wajen hidimar jama’a.
Ya rike mukamai daban-daban a matakin tarayya da jiha ciki har da: mataimakin shugaban majalisar gudanarwa ta hukumar FCDA da shugaban majalisar gudanarwa na Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika.
Haka kuma ya yi aiki a hukumar hukumar kula da kananan hukumomi, da ma’aikatar yada labarai da al'adu, inda ya kai matsayin darakta, rahoton The Nation.
Onyeabo ya jagoranci kamfanoni da dama da suka yi nasara, ya yi aiki da kamfanin Noble Order of Knights of St. Mulumba, kuma mamba ne a kungiyoyin mabiya darikar Katolika na Abuja da Enugu.
Kansila ta rasu kwana 12 bayan hawa mulki
A wani labarin, mun kawo maku cewa kansila mai wakiltar Mazabar C1 a karamar hukumar Ibeju-Lekki ta jihar Legas, Oluwakemi Rufai ta rasu.
Rahotanni daga Legas sun nuna cewa Oluwakemi Rufai ta rasu ne ne kwana biyu kafin ta cika makonni biyu da rantsar da ita a matsayin kansila.
Jam’iyyar APC reshen jihar Legas, ta bakin mai magana da yawunta, Seye Oladejo, ta bayyana matuƙar bakin cikinta da alhini bisa rasuwar Oluwakemi Rufai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng