Wata 1 da Rasuwar Buhari, Ma'aikatansa Sun Yi Hawaye, Sun Fadi Kyawawan Halayensa

Wata 1 da Rasuwar Buhari, Ma'aikatansa Sun Yi Hawaye, Sun Fadi Kyawawan Halayensa

  • Ma’aikatan gidan tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a Daura sun yi jimamin rasuwar mai gidansu bayan wata daya
  • Sannan ma'aikatan sun tuna kyawawan halayen marigayin inda suka ce kewayen gidan ya yi shiru tun bayan rasuwarsa
  • Sun bayyana shi a matsayin mai tausayi, aboki, kuma mai ziyartar iyalansu, inda ya ba su kulawa da goyon baya da yake raye

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu a ranar 13 ga watan Yulin 2025 a birnin London.

Wata guda bayan rasuwar Buhari, ma’aikatan gidansa a Daura sun ce suna ci gaba da ganin gibinsa a zuciyarsu kuma ba za su manta da shi ba.

Ma'aikata a gidan Buhari sun tuna mai gidansu
Ma'aikatan marigayi Buhari sun bayyana kyawawan halayensa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Ma'aikatan Buhari sun yaba halayensa

Rahoton Punch ya ce an birne tsohon shugaban kasar wanda ya rasu yana da shekara 82 a garin Daura da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan suka ce an san Buhari da tawali’u da hulɗa ta musamman, inda suka ce ba kawai mai aiki da su ba ne, amma aboki ne kuma jagora.

“Allah ya ji ƙan uban gidanmu, ya fi zama mana jagora da aboki kusa da iyalanmu wanda komai ya faru yana tare da mu.
“Wannan wata guda da tunanin ba zai dawo ba ya bayyana mana wani yanayi na shiru da babu komai a nan.
“Za mu yi kewarsa domin mun rasa aboki, jagora da mai aiki da mu. Zuwansa ya ba sanya mu alfahari."

- In ji wani ma’aikaci da ya nemi boye sunansa

Buhari ya samu yabo daga ma'aikatansa a Daura
Wata 1 da rasuwarsa, ma'aikatan Buhari sun yaba kyawawan halayensa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: AFP

'Yadda Buhari ya damu da mu' - Ma'aikacinsa

Wani ma’aikaci ya tuna yadda Buhari ke halartar abubuwan farin ciki ko jimami na ma’aikatansa, yana zaune na sa’o’i yana taya su da addu’a.

Ziyarar gidan Buhari ta nuna kabarinsa a harabar gidan, da aka lullube shi da kore da farin tutar Najeriya.

Kara karanta wannan

Jama'a sun 'dimauce da tankokin mai su ka fashe a Zariya

Kewaye da gidan ya koma yadda yake na al’ada, sai ƙarancin jami’an tsaro idan aka kwatanta da kwanaki bayan birne shi.

Wani makusancin iyalinsa ya ce ana shirin gudanar da addu’ar kwanaki 40, inda ake sa ran jama’a za su dawo Daura.

Ya ce:

“Bayan jana’iza da komawar iyali Kaduna, wurin ya yi shiru. Insha Allah, cikin kwanaki goma za su dawo domin addu’a."

Mazauna Daura sun bayyana shi a matsayin mutum mai ladabi, tsantseni, da kiyaye lokaci, wanda ke mutunta kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Rasuwarsa ta zama tunatarwa game da gajertar rayuwa da kuma kyawawan halaye da suka sa ya zama abin kauna a cikin gari da waje, cewar The Nation.

An fadi yadda Buhari ya hana tazarcen Obasanjo

Kun ji cewa tsohon Shugaban hukumar VON, Osita Okechukwu ya tuna baya kan neman wa'adin mulki na uku da Olusegun Obasanjo ya yi a 2006.

Osita Okechukwu ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen hana aukuwar hakan.

'Dan siyasar ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya tsaya tsayin daka wajen ganin shirin na Obasanjo bai yi nasara ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.