Abba Gida Gida Ya Yi wa Matasa Albishir, Ya Faɗi Tanadin da Gwamnatinsa Ta Yi Masu
- Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ba za ta bar matasan jihar a kara zube ba, suna zaman kashe wando ko ta'ammali da miyagun kwayoyi
- Gwama Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a matsayin wani bangare da bikin ranar matasa da duniya da aka gudanar a ranar Laraba
- Gwamnan ya ce daga cikin matakan gwamnatinsa ta dauka, akwai buɗe cibiyoyin koyar da sana’o’i don koyar da matasa da sama masu abin yi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da ci gaban matasa a jihar.
Gwamnan ya ce za a yi haka ne ta hanyar samar masu da ayyukan yi da kuma yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yayin bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2025.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

Source: Facebook
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafin Facebook, Gwamna Abba ya bayyana cewa matasa na da muhimmiyar rawa wajen sauya tattalin arzikin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin gwamnatin Abba kan matasan Kano
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta kaddamar da shirye-shiryen da su ka ba matasa damar samun ƙwarewa, dama, da goyon bayan da zai kai su yi nasara.
Ya bayyana cewa sake buɗe cibiyoyin koyar da sana’o’i a fannoni daban-daban ya riga ya 'dora dubunnan matasa a turbar dogaro da kai.

Source: Facebook
Gwamnan ya ƙara da cewa an samar da ayyukan yi kai tsaye a muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, noma da ayyukan jama’a.
Har ila yau, Gwamna Yusuf ya sanar da shirin sake buɗe cibiyar gyaran hali ta Kiru, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da rayuwar matasa masu ta'ammali da kwaya
'Za mu inganta fasahar matasa,' Abba
Dangane da ci gaban fasaha, Gwamnan ya yi nuni da kafa hukumar KASITDA da kuma shirya taron ƙasa da ƙasa kan fasaha da na'urorin zamani.
Ya bayyana cewa an samar da wannan ne domin mayar da Kano cibiyar ƙirƙira da haɓaka ƙwarewar fasaha, musamman a tsakanin matasa.
A cewarsa:
“A wannan Ranar Matasa ta Duniya, muna taya murnar jajircewa da basirar matasanmu. Gwamnatina za ta ci gaba da habaka rayuwarku ta hanyar samar da ayyukan yi, ilimi, fasaha, da kuma yaƙi da annobar miyagun ƙwayoyi.”
Ya yi kira ga shugabannin al’umma, malamai, iyaye, ɓangaren masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen gina Kano da za ta yi wa kowa dadi.
Abba ya tuna da iyalan 'yan wasan Kano
A baya, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasa 22 na Kano da suka rasu a mummunan haɗarin mota tallafin kuɗi da filaye.
Sanarwar da hadimin gwamnan, Ibrahim Adam ya fitar ta ce an ba wa iyalan tallafin kuɗi, ₦5,000,000 tare da filaye, a don su rage radadin wannan babban rashi da su ka yi.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗannan ’yan wasa na dawowa ne daga gasar da aka gudanar a jihar Ogun lokacin da haɗarin ya rutsa da su a ranar 31 ga Mayu, 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
