Ana Batun Rashin Lafiyar Tinubu, Gwamna Radda Zai Tafi Jinya domin Duba Lafiyarsa

Ana Batun Rashin Lafiyar Tinubu, Gwamna Radda Zai Tafi Jinya domin Duba Lafiyarsa

  • Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya shirya fita kasar waje domin yin hutu har na tsawon makonni uku
  • Radda zai fara hutun jinya na makonni uku daga 18 ga Agustan 2025 domin kula da lafiyarsa da yin gwaje-gwaje
  • A lokacin hutun, mataimakin gwamna, Faruk Lawal-Jobe zai jagoranci mulki, don tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Yayin da jihar Katsina ke fama da matsalolin rashin tsaro, Gwamna Dikko Umaru Radda zai tafi hutu.

Gwamna Radda zai fara hutun jinya na tsawon mako uku daga ranar 18 ga watan Agustan 2025 domin kula da lafiyarsa.

Gwamna Radda zai tafi ketare duba lafiyarsa
Gwamna Radda na Katsina zai tafi jinya ketare domin duba lafiyarsa. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu-Zango ya fitar a ranar Laraba a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jitar rashin lafiyar Tinubu da aka yada

Wannan mataki na Gwamna Radda na zuwa ne yayin da ake ta yada rade-radin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana fama da matsanancin jinya.

An kuma yada wasu rahotanni a daren ranar Talata 11 ga watan Agustan 2025 cewa Tinubu ya bar duniya wanda ya jawo maganganu a kasa.

Sai dai fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahoton da ake yadawa inda ta ce kwata-kwata ba gaskiya ba ne kuma yana cikin koshin lafiya.

Daga bisani, Tinubu ya shirya barin Najeriya a yau Alhamsi 14 ga watan Agustan 2025 domin zuwa kasashen Brazil, Japan da Dubai.

Tinubu zai ziyarci kasashen Brazil da Japan ne domin halartar wasu taruka da shugabannin duniya na wasu kwanaki.

Radda zai bar Najeriya domin kula da lafiyarsa

Radda ya bayyana aniyarsa ta shirin dawowa aikin mulki cikin kuzari da jajircewa bayan wannan hutun jinya da kuma duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu, yaran Bello Turji sun harbe mutane a Sokoto, sun sace mutum 16

Sanarwar ta ce:

“Ina son godewa kowa bisa kyawawan kalamai da goyon bayan da ake ba ni, Kula da lafiyata na da muhimmanci domin ci gaba da mulki yadda ya dace.
“Ina fatan dawowa bakin aiki da zarar na kammala binciken lafiyata domin kawo ci gaba ga al'ummar Katsina."

Kwamishinan ya bayyana cewa, don tabbatar da gudana da mulki cikin tsari, Mataimakin Gwamna Malam Faruk Lawal-Jobe zai jagoranci gwamnati a wannan lokaci.

Gwamna Radda ya nuna kwarin gwiwa cewa Lawal-Jobe zai gudanar da mulki da irin jajircewa da kulawa da shi ma yake nunawa a aikinsa.

“Muna tabbatar wa jama’a cewa dukkan shirye-shirye, tsare-tsare da ayyuka na ci gaba za su gudana ba tare da wani tangarda ba."

- Cewar sanarwar

Gwamna Radda zai kashe N1bn saboda ilimi

Mun ba ku labarin cewa majalisar zartarwa ta Katsina ta amince da kashe fiye da Naira biliyan daya don ayyuka a fannonin lafiya, ilimi da kuma makamashi.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

Gwamna Dikko Radda ya halarci taron majalisar na 10 ta yanar gizo yayin da aka yanke shawara kan ayyukan da za su amfani jihar.

An ware fiye da Naira miliyan 588 don sayen littattafai, Naira miliyan 500 don abinci mai gina jiki da kuma kudin sayo gidan sauro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.