Gwamna Ya Gaji da Hare Hare, Ya Roki Allah game da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci

Gwamna Ya Gaji da Hare Hare, Ya Roki Allah game da Masu Daukar Nauyin Ta’addanci

  • Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda, ya yi Allah wadai da kisan
  • Ya ce Allah SWT zai tona asiri ya kuma wulakanta masu daukar nauyin ‘yan bindiga, yana kira ga jama’a da su dage da addu’a
  • Ya yi alkawarin inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, ruwa da sadarwa a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Gwamna Dauda Lawal ya nuna damuwa kan ci gaba da kai hare-hare da yan bindiga ke yi a jihar Zamfara.

Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hare-hare a Kauran Namoda, inda ya yi Allah wadai da kisan.

Gwamna Dauda ya yi addu'o'i kan yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal ya roki Allah ya tozarta masu daukar nauyin ta'addanci. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Twitter

Gwamna ya ziyarci wuraren da aka kai hari

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Gwamnan ya ce duk da cewa bai kasance a jihar lokacin harin ba, ya aika Mataimakinsa da tawaga mai karfi domin jajantawa da tantance asarar da aka tafka, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar ta shafi garuruwa biyar da suka fi fuskantar hare-haren, wato Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru da Tambarawa, inda mazauna suka yi asarar rayuka.

Ya ce bayan dawowarsa daga tafiya, ya ziyarci al’ummomin da abin ya shafa don ganin halin da suke ciki da kuma yi musu ta’aziyya kai tsaye.

Ya ce:

“Ina nan a Banga domin yin ta’aziyya kan harin ‘yan bindiga da ya faru kwanan nan, wanda ya jefa jama’a cikin bakin ciki."

Gwamna Lawal ya yi addu'o'i ga yan bindiga

Gwamna Lawal ya yi Allah wadai da hare-haren, yana kiran maharan “makiyan zaman lafiya” masu nufin tsoratar da jama’a da tayar da rikici a yankin.

Ya roƙi Allah ya tona asirin masu daukar nauyin hare-haren, ya kuma wulakanta su, yana kira ga jama’a su dage da addu’a.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu

Dauda Lawal ya sha alwashin ci gaba da daukar matakan gaggawa domin kare dakile hare-haren yan bindiga wanda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyin al'umma.

Dauda Lawal ya nuna damuwa kan hare-haren yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal ya roki Allah kan hare-haren yan bindiga a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Alkawarin da Dauda Lawal ya yi ga al'umma

Gwamna Dauda Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yaki da ‘yan bindiga tare da ƙirƙirar sababbin dabaru da haɗin gwiwa.

Sarkin Kauran Namoda, Dr. Sunusi Ahmad, ya yaba da ziyarar, yana cewa ta nuna kulawa da damuwar gwamnati kan matsalar tsaro.

Gwamnan ya kuma sanar da shirin inganta hanyoyi, wutar lantarki, ruwan sha da sadarwa domin tallafawa yankunan da abin ya shafa.

'Yan majalisa sun yi korafi kan matsalar tsaro

A wani labarin, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Zamfara ta nuna damuwarta kan yadda 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

'Yan majalisar dokokin sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda Gwamna Dauda Lawal yake tafiyar da al'amuran tsaro a fadin jihar.

Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da gwamnan gefe, ta dauki matakan kawo karshen ayyukan 'yan bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.