Ana Batun Sulhu, Yaran Bello Turji Sun Harbe Mutane a Sokoto, Sun Sace Mutum 16

Ana Batun Sulhu, Yaran Bello Turji Sun Harbe Mutane a Sokoto, Sun Sace Mutum 16

  • Wasu yaran Bello Turji, karkashin jagorancin Kallamu, sun kai farmaki jihar Sokoto inda suka kashe mutum daya tare da sace asu 16
  • Wannan sabon hari ya jefa shakku kan batun sulhu da Bello Turji, yayin da ake zargin yana amfani da hakan don kara karfin rundunarsa
  • Rahotanni sun nuna wasu yaransa na ci gaba da safarar makamai a tsakanin Najeriya da Nijar, duk da tattaunawar sulhu da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Da alama maganar sulhu da Bello Turji za ta bi ruwa yayin da wasu yaransa suka kai sabon hari kauyen Garki da ke jihar Sokoto.

An ce 'yan ta'addan masu biyayya ga hatsabibin dan bindigar sun kashe mutum daya sannan suka yi garkuwa da wasu 16 a sabon harin.

Kara karanta wannan

An kashe kusan N50trn: Manyan ayyuka 16 da Tinubu ya yi bayan cire tallafin mai

'Yan bindiga da ke biyayya ga Bello Turji sun harbe mutane a Sokoto, sun sace wasu 16
Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto duk da ana tattaunawar sulhu. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yaran Bello Turji sun kai hari Sokoto

Majiyoyi daban daban sun shaida wa Zagazola Makama cewa wani babban na-hannun damar Bello Turji, mai suna Kallamu ne ya jagoranci harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Kallamu ya jagoranci tawagar 'yan ta'addar a yammacin ranar Talata, inda suka bude wuta kan mai uwa da wani lokacin da suka shiga kauyen.

Wani mazaunin kauyen Garki ya shaida wa manema labarai cewa:

"Sun shigo garin da yawansu, suka tafi da mutane 16 da dabbobi masu yawa bayan sun kashe mutum daya. Sun kuma harbe mutane uku wadanda yanzu suke kwance a asibitin Sokoto."

"Bai kamata a yarda da Bello Turji ba"

Wannan harin dai na zuwa ne duk da cewa ana batun sulhu tsakanin Bello Turji da wasu wakilan gwamnati.

Sai dai wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wannan sabon harin na iya zama wata alama ta baraka a sansanin Bello Turji.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina, an ceto mutane

Wata majiyar tsaro ta ce:

"Bello Turji ya dade yana amfani da wannan batun sulhun yana kara karfin rundunarsa ta karkashin kasa, kuma hakan na bashi damar mamayar wasu yankuna.
"Bai kamata a yarda da shi ko abin da zai ce ba saboda a duk lokacin da ake sulhu da shi, to za ka ga yaransa suna ci gaba da kai hari, suna kashe mutane da garkuwa da wasu."
Mata majiyar tsaro ta yi ikirarin cewa Bello Turji na amfani da wannan tattaunawar sulhun don kara karfin rundunarsa
Hatsabibin jagoran 'yan bindiga, Bello Turji da ya addabi Arewa maso Yamma. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Yaran Bello Turji sun shiga safarar makamai

Majiyar ta kuma kara da cewa wasu bayanan sirri sun nuna cewa har yanzu Bello Turji na gudanar da ayyukan ta'addanci a yankin Isa, Sabon Birni da Goronyo.

Ya kuma kara da cewa an gano yaran Bello Turji sun fadada ayyukansu zuwa safarar makamai da mutane a tsakanin iyakokin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

Batun sulhu tsakanin Bello Turji da gwamnati dai ya jawo sabani sosai a tsakanin wasu malaman Musulunci na Arewa.

Yayin da wasu malaman ke ganin sulhun na da kyau la'akari da ganin barnar da 'yan ta'addar ke yi, wasu malaman kuma na ganin hakan kuskure ne, kuma bai kamata a yafe wa Turji ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai hari 'Gidansu Atiku,' sun yi garkuwa da mata

Turji: Cacar baki tsakanin Asada da Albaniy

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Malam Murtala Asada ya mayar da martani mai zafi ga Sheikh Adam Muhammad Albaniy kan sukar sulhu da Bello Turji.

Murtala Asada ya ce ya sha ba jami’an tsaro bayanai har aka kai wa Bello Turji hari, lamarin da ya fusata rikakken dan bindigar matuka.

Ya bayyana cewa Bello Turji ya taba yin bidiyo yana masa barazana saboda bayanan da suka kai ga kisan mutanensa, wanda ya ke ganin bai kamata Albaniy yana sukar sulhun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com