Girma Ya Fadi: Na'ibin Limamin Juma'a Ya Shiga Hannu kan Zargin Hada Baki da 'Yan Bindiga
- Dubun wani malamin musulunci kuma na'ibin limamin masallacin Juma'a ta cika kan zargin hada baki da 'yan bindiga a jihar Sokoto
- Jami'an tsaro sun samu nasarar cafke na'ibin limamin ne bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansa duk da yana malamin addini
- Hakazalika an samu miliyoyin kudi a asusunsa wadanda ake zargin ya same su ne sakamakon alakar da yake yi da 'yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Jami’an tsaro sun kama Sirajo Ahmad Dan Liman, na'ibin babban limamin masallacin Juma’a a jihar Sokoto kan zargin aiki da 'yan bindigan.
Sirajo Ahmad Dan Liman wanda shi ne Na'ibin limamin masallacin Juma'a na Kangiye, a mazabar Atakwanyo, ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto, ya shiga hannu ne bisa zargin haɗa baki da ’yan bindiga.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na'ibin Liman ya shiga hannun jami'an tsaro
Majiyoyi bayyana cewa cewa binciken lelen asiri ya gano alakar Sirajo da samar da babura da sauran muhimman kayayyaki ga ’yan bindiga da ke aiki a yankin iyakar Tangaza–Jamhuriyar Nijar.
Jami’an tsaron sun gano kudi har Naira miliyan 47 a asusun bankinsa, waɗanda ake kyautata zaton kudaden haramun ne daga hulɗarsa da ’yan ta’addan.
Bincike ya ƙara gano cewa Sirajo shi ne shugaban wata jam’iyyar siyasa a mazabar Atakwanyo, kuma sakataren ƙungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa a ƙaramar hukumar Gwadabawa.
Majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya shahara wajen yin wa’azi a Kangiye a lokacin watan Ramadan.
Hakazalika yana maye gurbin mahaifinsa babban limami wajen jagorantar sallar Juma’a da yin huduba idan ba ya nan.
Hukumomi sun bayyana cewa kama shi na daga cikin matakan da ake ci gaba da ɗauka don rusa hanyoyin samun kuɗi da na kayan aiki da ke tallafawa ayyukan ta’addanci a Sokoto da jihohi makwabta.

Asali: Original
Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga
- Katsina: Basaraken da ake zargi da yi wa 'yan ta'adda jagora ya fada komar jami'an tsaro
- Katsina: Yan siyasa, sarakuna sun zauna da yan bindiga, an kafa sharuda 20 na zaman lafiya
- Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai hari 'Gidansu Atiku,' sun yi garkuwa da mata
- Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga bayan an gwabza fada a Katsina
- 'Babban bala'in da ke tunkaro mu': Shehi ya faɗi abin da Bello Turji ya faɗa masa
'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka jami'an tsaro a jihar Zamfara.
Jami'an tsaron sun rasa rayukansu ne bayan 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a kauyen Adabka da ke karamar hukumar Bukkuyam.
A yayin kwanton baunan da 'yan bindigan suka shirya, an kashe jami'an tsaro guda 10 ciki har da 'yan sanda, jami'an CJTF da jami'an rundunar Askarawan Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng