Cikakkun Sunaye: Gwamna Inuwa Zai Kirkiri Sababbin Kananan Hukumomi 13 a Gombe

Cikakkun Sunaye: Gwamna Inuwa Zai Kirkiri Sababbin Kananan Hukumomi 13 a Gombe

  • Gwamnatin Gombe ta tura kudirin kafa sababbin gundumomin ci gaba 13, da za a ciro daga kananan hukumomi 11 da ake da su
  • Daraktan yada labaran gwamnati, Ismaila Uba Misili ya ce gungumomin za su magance matsalolin tsaro, ilimi, kiwon lafiya
  • An fitar da sunayen sababbin gundumomin 13 da hedikwatocinsu, tare da shirin da aka yi na nada masu kwamitocin wucin gadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta aika kudurin doka ga majalisar dokokin jihar na kirkirar sababbin gundumomin ci gaba guda 13 (LCDAs).

A cikin daftarin kundin da aka aika wa majalisar, gwamnati ta ce za a ciro sababbin gundumomin daga kananan hukumomi 11 da ake da su a jihar.

Gwamnatin Inuwa Yahaya ta gabatar da kudurin kirkirar sababbin kananan hukumomi 13 a Gombe
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya zai kirkiri sababbin kananan hukumomi 13. Hoto: @IsmailUMisilli
Asali: Facebook

Za a kirkiri gundumomin ci gaba 13 a Gombe

Babban daraktan watsa labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misili ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ismaila Uba Misili ya sanar da cewa wannan matakin na daga cikin kokarin Gwamna Inuwa Yahaya na ƙarfafa harkokin mulki daga tushe.

"Hakan dai ya yi daidai da ƙudurin Gwamna Inuwa Yahayan na ƙoƙarin kusantar da mulki ga jama’a, da inganta yadda ake hidimtawa al'umma da demokraɗiyya don damawa da kowa da ƙarfafa haɗin kai a faɗin jihar.
"An tsara gundumomin ci gaban (LCDAs) a matsayin sassan gudanarwa na kananan hukumomin da ake da su."

- Ismaila Uba Misili.

Manufar kirkirar LCDAs 13 a jihar Gombe

Daraktan watsa labaran ya ce sababbin gundumomin za su taka muhimmiyar rawa wajen magance muhimman matsalolin cikin gida a fannonin tsaro, ilimi da kiwon lafiya.

Sauran bangarorin da za su magance sun hada da samar da ababen more rayuwa da kuma kyautata harkokin zamantakewa, musamman a yankunan karkara da wadanda aka bari a baya.

Ismaila Misili ya kuma ce:

"Haka kuma LCDAs ɗin za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautun gargajiya da shugabannin al’umma don wanzar da zaman lafiya, inganta ci gaba da magance matsalolin tsaro da suke kunno kai, daidai da tanade-tanaden dokar masarautu ta Jihar Gombe (da aka yiwa kwaskwarima)."

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun kai karar Gwamna Dauda kan matsalar rashin tsaro

Gombe: Jerin gundumomin ci gaba 13

Sababbin gundumomin ci gaban guda 13 tare da hedkwatocinsu da aka gabatar su ne kamar haka:

  1. Akko ta Arewa (Mai Hedkwata a Amada)
  2. Akko ta Yamma (Mai Hedkwata a Pindiga)
  3. Balanga ta Kudu (Mai Hedkwata a Bambam)
  4. Billiri ta Yamma (Mai Hedkwata a Tal)
  5. Dukku ta Arewa (Mai Hedkwata a Malala)
  6. Funakaye ta Kudu (Mai Hedkwata a Tongo)
  7. Gombe ta Kudu (Mai Hedkwata a Bolari)
  8. Kaltungo ta Gabas (Mai Hedkwata a Wange)
  9. Kwami ta Yamma (Mai Hedkwata a: Bojuɗe)
  10. Nafaɗa ta Kudu (Mai Hedkwata a Birin Fulani)
  11. Pero-Chonge (Mai Hedkwata a Filiya)
  12. Yamaltu ta Gabas (Mai Hedkwata a Hinna)
  13. Yamaltu ta Yamma (Mai Hedkwata a Zambuk)
Gwamnatin Gombe za ta kafa kwamitocin wucin gadi ma sababbin gundumomin ci gaba 13 kafin zaben ciyamomi
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya a taron gwamnonin Arewa. Hoto: @IsmailUMisilli
Asali: Facebook

Za a kafa kwamitocin gudanarwa kafin zabe

Don tabbatar da an aiwatarwa komai cikin sauƙi, sanarwar ta ce ƙudurin dokar ya tanadi kafa kwamitocin gudanarwa na wucin gadi da za su gudanar da harkokin kowace gundumar ci gaba kafin a gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wanda ake zargi da kashe jami'in NSCDC ya yi mummunan ƙarshe bayan cafke shi

"Za a fitar da tsarin da ya dace tare da fayyace jadawalin ayyukansu, da tsarin samar da ma'aikata da kasafin kuɗi don tabbatar da ingancinsu tun daga farko.
"Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ƙira ga Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta gaggauta duba kudirin tare da bashi kulawar data dace.
"Ya kuma yi ƙira ga al'ummar jihar su goyi bayan wannan tsari na hangen nesa, wanda ke ƙara ƙarfafa matakin Jihar Gombe a matsayin jagora wajen gudanar da mulki da samun ci gaban ƙasa."

- Ismaila Uba Misili.

Alkawarin Gwamnan Gombe ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Gwamnan ya ba shugaban kasar tabbacin cewa al'ummar jihar Gombe za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada masa kuri'a a zaben mai zuwa.

Inuwa Yahaya ya ce Tinubu ya zuba jari sosai a harkar kiwo, wanda ya haifar da ci gaba, samar da aiki da inganta rayuwar al'umma musamman a Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com