Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma na Watanni 3

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma na Watanni 3

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku
  • Wannan dakatarwa ta biyo bayan koarafin da kansilolin karamar hukumar guda tara su ka shigar a gaban majalisa domin a duba kokensu
  • Daga cikin abubuwan da su ka zargi shugaban karamar hukumar da shi akwai cefanar da kadarorin gwamnati da kuma takin zamani

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Majalisar dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u bayan shawarar kwamitin bincikenta karkashi Lawan Hussaini Dala.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon Lawan Hussaini Dala ya sanar da cewa sun dauki matakin ne saboda zarge-zargen almundahana da amfani da dukiyar jama’a ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanar da kama shugaban kungiyar ta'addanci da ta bulla a jihohin Arewa

Taswirar jihar Kano
Majalisa ta dakatar da Shugaban karamar hukuma a Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tribune Online ta wallafa cewa an wasu daga cikin kansilolin karamar hukumar Rano guda tara ne su ka shigar da korafi gaban majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta dakatar da shugaban karamar hukumar Kano

Daily Post ta wallafa cewa ana zargin shugaban karamar hukumar da kashe kuɗin gwamnati ba bisa ka’ida ba, sayar da shaguna, da karkatar da taki da aka tanadar wa manoman yankin.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa kwamitin ya yi amfani da Sashe na 128 na Kundin Tsarin Mulki da kuma Sashe na 55 (1–6) na Dokar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano ta 2006 wajen dakatar da shi.

Ya kuma ba da shawarar a dakatar da shi na tsawon watanni uku domin gudanar da cikakken bincike a kan zargin da ake yi masa.

Haka kuma za a gaggauta gabatar da bayanan kuɗin karamar hukumar Rano na shekarar 2025 da kuma nada mataimakinsa a matsayin mukaddashin Shugaba.

Dala ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ruwan mukamai a hukumomin tarayya ana jita jitar ciwo

“Bayan dogon tattaunawa, majalisa ta amince da shawarwarin kwamitin, wanda hakan ya tabbatar da dakatar da shugaban tare da sanya karamar hukumar a ƙarƙashin kulawar wucin-gadi.”

Majalisa ta zauna kan batun shugaban karamar hukumar

Daya daga cikin ‘yan jaridu da suka halarci zaman majalisar, Kamal Kurna, ya shaida wa Legit cewa ba a ga shugaban karamar hukumar Rano a zaman majalisar ba.

Amma Shugaban masu rinjaye na majalisa, Lawan Hussaini Dala, ya shaida wa ‘yan jaridu cewa an yi zama da shugaban karamar hukumar Rano, Muhammad Naziru Ya’u.

Ya kara da cewa duk da cewa shugaban ya karyata dukkannin zarge-zargen, majalisa ta amince da dakatar da shi har sai an kammala bincike.

Majalisar dokokin Kano
Majalisa za ta binciki Shugaban karamar hukuma a Kano Hoto: UGC
Source: Facebook

A halin yanzu, dakataccen shugaban karamar hukumar bai ce komai ba a kan matakin dakatar da shi da majalisar ta dauka yayin da bincike ke ci gaba kan zarge-zargen da ake masa.

'Yan siyasa sun zauna da 'yan sandan jihar Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa jagororin jam’iyyun siyasa sun amince da bin ka’idojin gudanar da zabe cikin lumana.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun kai karar Gwamna Dauda kan matsalar rashin tsaro

Sun yi alkawarin ne bayan sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Bompai, ranar Talata, yayin da ake shirin zaben cike gurbi.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sanya hannu kan yarjejeniyar zai ƙara tabbatar da tsaro, zaman lafiya gabnin zaben ranar Asabar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng