Magana Ta Kare, Bidiyon Shugaba Tinubu Ya Bayyana ana tsaka da Jita Jitar ba Shi da Lafiya
- Jita-jitar da ke ci gaba da yawo kan lafiyar shugaban kasa ta zo karshe da bidiyon Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a yau Laraba
- Hadimin shugaban kasa, Abdul'aziz Abdul'aziz ya fitar da faifan bidiyon da ke nuna Tinubu ya isa dakin taron Majalisar Zartarwa (FEC)
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na cikin wadanda suka halarci taron a Aso Rock
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - A 'yan kwanakin nan, ana ta yada jita-jitar cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na fama da rashin lafiya shi yasa aka daina ganinsa a bainar jama'a.
Fadar shugaban kasa ta fito ta musanta wannan jita-jita, tana mai cewa cewa rashin ganin Tinubu ba abin damuwa ba ne don yana da yancin aiki daga gida.

Kara karanta wannan
Da gaske ba shi da lafiya? Gwamna ya fadi halin da ya tarar da Shugaba Tinubu a Aso Rock

Source: Facebook
An saki bidiyon Shugaba Tinubu a Aso Rock
A yau Laraba, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin jaridu, Abdul'aziz Abdul'aziz ya wallafa bidiyon fitowar Bola Tinubu zuwa wurin taro a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A faifan bidiyon, an ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fito domin halartar taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a Aso Rock yau Laraba.
"Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa dakin taron majalisar zartarwa ta tarayya a yau Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025," in ji Abdul'aziz.
A faifan bidiyon dai alamu sun nuna Tinubu lafiyarsa kalau, domin an ga ya shigo dakin taron kuma ya wuce wurin zamansa, ya tsaya an yi taken Najeriya kafin ya zauna.
Shettima da ministoci sun halarci taron FEC
Legit Hausa ta gano cewa taron dai na gudana ne a zauren majalisar zaratarwa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.

Kara karanta wannan
Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock
Sauran sun hada da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Mafi akasarin ministocin gwamnatin Shugaba Tinubu sun halarci taron na yau Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
FEC ta yi jimamin rasuwar Audu Ogbeh
Kafin fara taron, sakataren gwamnatin tarayya, Senator George Akume ya sanar da Majalisar rasuwar tsohon ministan harkokin noma, Cif Audu Ogbeh.
Ogbeh wanda ya rasu a makon jiya ya kasance tsohon shugaban PDP ta kasa kuma ministan noma a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
Bayan haka majalisar zartarwa ta yi shiru na minti daya domin karrama dattijon da ya rasu wanda Akume ya bayyana a matsayin dan kishin kasa.
Gwamna Soludo ya tabbatar da lafiyar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cikin koshin lafiya.
Gwamnan na Anambra ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Bola Tinubu yayin da ya kai masa ziyara a fadar shugaban kasa ranar Talata.
Soludo ya ce ya hadu da shugaban kasa kuma yana cikin koshin lafiya, sannan yana ci gaba da karbar baki da wasu aikace-aikace na ofishinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng