Gwamna Ya Sanar da Kama Shugaban Kungiyar Ta'addanci da Ta Bulla a Jihohin Arewa
- Gwamnan jihar Neja, Muhammed Umaru Bago ya tabbatar da labarin cafke shugaban kungiyar yan ta'addan nan ta Mahmuda, Abubakar Abba
- Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Balogi Ibrahim ya fitar, ya ce tuni aka wuce da shi Abuja don ci gaba da bincike
- A kwanakin baya ne aka samu labarin cewa jami'an hukumar DSS sun cafke dan ta'addan a garin Wawa da ke karamar hukumar Borgu a Neja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da cafke shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Mahmuda, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ake tsoro sosai a Arewacin Najeriya.
A watannin da suka gabata ne kungiyar Mahmuda ta bulla a Najeriya, kuma mayakanta suka fara kai hare-hare a Neja da Kwara da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

Source: Facebook
Leadership ta tattaro cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Mohammed Bago na jihar Neja, Balogi Ibrahim ya fitar, ya tabbatar da kama shugaban Mahmuda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya tabbatar da kama shugaban Mahmuda
Balogi Ibrahim ya bayyana cewa an kama shugaban kungiyar ta’addancin mai suna Abubakar Abba a garin Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Kakakin gwamnan ya kuma tabbatar da cewa tuni aka tura shi babban birnin tarayya Abuja domin ci gaba da bincike.
Balogi ya ce Gwamna Bago ya bayyana wannan nasara a matsayin alamar jajircewar Shugaba Bola Tinubu wajen tabbatar da tsaron rayuka da walwalar ’yan Najeriya.
Yadda DSS ta cafke jagoran 'yan ta'addan
Idan ba ku manta ba kwankin baya, an rahoto cewa dakarun hukumar tsaron farin kaya watau DSS sun damke shugahan Mahmuda, Abubakar Abba.
Wasu rahotanni sun ce DSS ta kama shugaban kungiyar Mahmuda ne a kusa da iyakar Jamhuriyar Benin.
Gwamnatin jihar Neja ya yabawa Bola Tinubu
Da yake tabbatar da wannan nasara, kakakin gwamnan Neja, Balogi Ibrahim ya ce:
“Eh, gaskiya ne. Zan iya tabbatar da cewa DSS ta kama shugaban Mahmuda, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta’addanci mafi hatsari a Afirka ta Yamma, Abubakar Abba.”
“An kama shi da ransa ne a wani samame da dakarun DSS suka gudanar bayan sun samu sahihan bayanan sirri. Wannan babbar nasara ce a gare mu a matsayin al’umma da gwamnati.
"Shugaba Tinubu ya cancanci yabo bisa wannan labari mai daɗi, kuma hakan ya kara nuna jajircewar shugaban kasa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da inganta rayuwar ’yan Najeriya.”

Source: Facebook
Sojoji sun ragargaji yan ta'adda a jihar Neja
A wani labarin, kun ji cewa jami'an sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga masu yawa yayin wani artabu da suka yi a jihar Neja.
An ruwaito cewa hukumar DSS ce ta samu bayanan sirri kan shirin yan ta'addan na kai hari kan jama'a, nan take suka sanar da sojoji wadanda suka dauki mataki nan take.
A cewar majiyoyin, musayar wuta ta barke tsakanin dakarun da tsagerun a ranar Juma’a, wanda hakan ya haifar da kisan akalla 'yan ta'adda 45.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
