Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Mika Bukatarsa ga Rundunar Sojojin Sama
- Babagana Umara Zulum, na son rundunar sojojin sama ta murkushe mayakan kungiyoyin ta'addanci na Boko Haram da ISWAP
- Farfesa Zulum ya yi kira ga rundunar da ta tura jiragen yaki maboyar 'yan ta'adda da ke da wahalar shiga ga dakarun sojojin kasa
- Gwamna Zulum ya kuma yi alkawarin ba da goyon bayan da ake bukata don samun nasarar ayyukan jami'an tsaro a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika kokon bararsa ga rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) kan mayakan Boko Haram da ISWAP.
Gwamna Zulum ya bukaci rundunar da ta tura jiragen yaki domin kawar da mayakan Boko Haram da ISWAP daga wuraren da ke da wahalar shiga kamar tafkin Chadi, dajin Sambisa, Timbuktu Triangle da tsaunukan Mandara.

Source: Twitter
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin babban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Hassan Bala Abubakar, a Maiduguri ranar Talata, 12 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum na son a kakkabe Boko Haram
Gwamna Zulum ya ce waɗannan wurare na yi wa sojojin kasa matukar wahalar tsarewa yadda ya kamata.
"Duk da irin gudunmawar da NAF ta bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a Borno, har yanzu muna buƙatar ƙarin ƙarfin sojojin sama a yankin da muke da alhakin tsaro, musamman a sansanonin ‘yan ta’adda da ke wuraren da ba a iya shiga cikin sauki."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamna Zulum ya yaba da tura jirage marasa matuƙi da sauran kayan aiki, tare da yin alkawarin ba da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da nasarar ayyukan jami'an tsaro.
Haka kuma, ya jinjinawa haɗin gwiwa tsakanin NAF da sauran hukumomin tsaro wajen samun nasarori a yaƙin kawar da ‘yan ta’adda a baya-bayan nan, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Source: Facebook
Shugaban sojojin sama ya yabi Zulum
A nasa jawabin, Air Marshal Abubakar ya yaba da irin jagorancin Gwamna Zulum da kuma tsarin “Borno Model” na dawo da ‘yan ta’adda cikin jama’a.
Sojan ya bayyana cewa wannan hanya ta zama nasarar magance ta’addanci ba tare da amfani da yaƙi kai tsaye ba.
Ya ce shirin tuba, ajiye makamai da dawo da su cikin jama’a, wanda ya fi mayar da hankali kan kai zuciya nesa da sulhu maimakon hukunci, ya inganta tsaro a fadin Borno da Arewa maso Gabas baki ɗaya.
Air Marshal Abubakar ya ƙara da cewa rundunar sojojin sama ta Operation Hadin Kai ta ƙara zafafa ayyukanta a bana fiye da yadda aka taɓa gani a baya.
'Yan Boko Haram sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe jami'an sojoji a wani hari da suka kai a Borno.
'Yan ta'addan sun kai harin ne a kauyen Kirawa da karamar hukumar Gwoza, inda suka kuma yi awon gaba da wata daliba.
Harin na 'yan ta'addan ya sanya mutanen yankin tserewa zuwa kasae Kamaru domin tsira da rayukansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


