Da Gaske ba Shi da Lafiya? Gwamna Ya Fadi Halin da Ya Tarar da Shugaba Tinubu a Aso Rock
- Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cikin koshin lafiya
- Soludo ya fadi haka ne ranar Talata, 12 ga watan Agusta, 2025 bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Sabanin rade-radin da ake yadawa game da rashin lafiyar Tinubu, Soludo ya ce ya tarar da shugaban kasa cikin koshin lafiya, yana karbar baki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - A jiya Talata ne gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Wannan ziyara ta zo a daidai lokacin da ake rade-radi game da lafiyar shugaban ƙasar, bayan ya shafe sama da mako guda ba a gan shi bainar jama’a ba.

Kara karanta wannan
Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock

Source: Twitter
Wane hali Bola Tinubu ke ciki?
Daily Trust ta rahoto cewa yayin da yake magana da ’yan jarida bayan ganawa da Tinubu a ofishinsa, Soludo ya ce shugaban ƙasar “yana cikin koshin lafiya sosai.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Shugaban ƙasa, Bola Tinubu yana cikin farin ciki, yana cikin ƙoshin lafiya, yana karɓar baƙi da sauran aikace-aikace, tattaunawar da muka yi ta kasance mai daɗi," in ji Soludo.
Baya ga Soludo, gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, Sanata Aliyu Wadada sun kai ziyara ga Shugaba Tinubu a Aso Rock.
Haka zalika an hangi Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun a fadar shugaban kasar domin ganin Shugaba Tinubu.
Gwamna Soludo ya aika sako ga 'yan adawa
Gwamna Soludo, wanda ke neman tazarce a ranar 8 ga Nuwamba, 2025 ya yi kira ga ’yan siyasa masu ra’ayin ci gaba su kafa “babbar haɗaka” don marawa Tinubu baya.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki
Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya zama dole “ba wai kawai don bunƙasa dimokuraɗiyya ba, har ma don ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewa na ƙasarmu.”
Duk da ya ƙi bayyana cikakken bayanin tattaunawar da suka yi, Soludo ya ce:
“Na yi farin cikin haduwa da shi; ganawar da muka yi ta kasance mai daɗi ƙwarai.”

Source: Twitter
Meyasa Soludo ya sa tambarin Tinubu a hula?
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa, a matsayinsa na dan jam’iyyar APGA, ya sa hula mai ɗauke da tambarin Tinubu, Soludo ya ce hular tana cikin hulunan da aka yi lokacin da Tinubu ya ziyarci Anambra.
Ya jaddada cewa akwai bukatar duka jam'iyyun siyasa sa ke son kawo ci gaba su hada kansu, domin inganta dimokuradiyya, tattalin arziki da zamantakewar al'umma.
Fadar shugaban kasa ta yi magana
A baya, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa Bola Tinubu na fama da rashin lafiya shiyasa aka daina ganinsa a bainar jam'a.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da bayanai, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu na nan lafiyarsa kalau, yana gudanar da aikinsa.
Onanuga ya kuma kare shugaban kasa kan zargin rashin halartar taruka da wasu ayyuka a bainar jama'a, yana mai cewa Tinubu na da yancin yin haka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng