Matatar Dangote Ta Sake Sauya Farashin Fetur Karo na 2 cikin Kwana 5
- Za a samu sauki kan yadda ake sayan man fetur a gidajen mai a Najeriya bayan matatar Dangote ta rage farashin kowace lita
- Matatar ta hamshakin attajirin ta sanar da yin ragin N30 kan kowace litar man fetur da take sayarwa ga 'yan kasuwa masu dillancinsa
- Hakazalika matatar Dangote ta bayyana za ta fara amfani da manyan motoci masu aiki da iskar gas (CNG) don rabon fetur a fadin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Matatar hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ta rage farashin da take sayar da litar man fetur ga 'yan kasuwa a Najeriya.
Matatar ta rage N30 kan farashin kowace lita da take sayarwa 'yan kasuwa, wanda hakan ya sa ya ragu daga N850 ya dawo N820.

Asali: Getty Images
Babban jami’in sadarwar matatar, Anthony Chiejina, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya amince da kashe N16.7bn bayan ambaliyar ruwa ta yi barna a Neja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Anthony Chiejina bayyana cewa sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Agustan 2025.
Babban jami'in sadarwar ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar matatar wajen tallafa wa ci gaban ƙasa, tare da tabbatar da samar da kayayyakin mai ba tare da katsewa ba.
"Matatar Dangote na sanar da rage farashin fetur da N30, daga N850 zuwa N820 kan kowace lita, wanda zai fara daga ranar 12 ga Agusta, 2025."
"A matsayin wani bangare na jajircewarmu ga ci gaban ƙasa, muna tabbatar wa jama’a cewa za mu ci gaba da samar da kayayyakin mai ba tare da tangarda ba."
- Anthony Chiejina
Matatar Dangote za ta fara rarraba mai
Bugu da ƙari, ya bayyana cewa daga ranar 15 ga watan Agusta, kamfanin zai fara tura manyan motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin rarraba mai a faɗin Najeriya, rahoton The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan
Sauki ya fara isowa ga talakawa bayan Dangote ya canza farashin litar fetur a Najeriya
"Bisa ga jajircewarmu wajen inganta ayyuka da samar da hanyoyin makamashi masu dorewa, matatar Dangote za ta fara tura manyan motoci 4,000 masu amfani da CNG don rarraba mai a duk faɗin ƙasar nan, wanda zai fara daga 15 ga watan Agusta, 2025."
- Anthony Chiejina

Asali: UGC
Karanta wasu labaran kan Dangote
- Dangote ya bude wa 'yan Najeriya guraben neman aiki a kamfaninsa
- Dangote ya fara cin karo da matsala, ana fargabar zai jawo karancin mai
- Dangote zai saka matatarsa a kasuwa domin jama'a su mallaki hannun jari
- Dangote zai bude sabon kamfanin siminti, mutane za su samu aiki a Côte d’Ivoire
Abubakar Mika'il ya yaba da matakin matatar Dangote na rage farashin man fetur a Najeriya.
"Wannan abin a yaba ne, muna fatan farashin man fetur ya ci gaba da saukowa domin jama'a su samu sauki."
"Zuwan wannan matatar muna fatan ya zame mana alheri a kasar nan."
- Abubakar Mika'il
'Yan kasuwa sun rage farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan kasuwa da ke shigo da man fetur daga waje sun rage farashin da suke sayar da kowace lita.
'Yan kasuwan sun fara sayar da fetur din a kasa da farashin matatar Dangote da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).
A wasu wuraren da ake rarraba man fetur din, ana sayar da shi kasa da N820 wanda shi ne farashin da matatar Dangote take sayarwa 'yan kasuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng