Hukumar EFCC Ta Saki Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwa, An Samu Bayanai
- Hukumar EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal bayan ya shafe sama da awanni 24 a tsare
- EFCC ta tsare Tambuwal ne tun jiya Litinin yayin da ya amsa gayyatar da aka masa kan zargin cire makudan kudi N189bn lokacin da yake gwamna
- Wani jami'in bincike a EFCC ya tabbatar da cewa an ba da belin Aminu Tambuwal amma za a ci gaba da bincike kan zarge-zargen da ake masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'adi watau EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan jami'an EFCC sun tsare Tambuwal a ofishinsu yayin da ya amsa gayyatar da suka aika masa ranar Litinin.

Source: Facebook
Wasu makusantan Sanata Aminu Tambuwal sun tabbatar da sakinsa ga BBC Hausa, kuma yanzu haka yana gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda EFCC ta tsare Sanata Aminu Tambuwal
Hukumar EFCC ta tsare Aminu Tambuwal ne kan zarge-zargen ciremakudan kudi masu yawa da ake zargin sun kai Naira biliyan 189 a lokacin yana gwamnan Sakkawato.
Tambuwal ya isa hedkwatar EFCC da misalin ƙarfe 11:16 na safe a ranar Litinin, amma daga baya aka tsare shi bayan rahotanni sun ce ya kasa bayar da amsoshin tambayoyin da aka yi masa.
Wani jami’in bincike na musamman a hukumar EFCC, ya tabbatar da sakinsa ga Daily Trust yau Talata, ya ce an ba da belinsa bayan ya cika duka sharudda.
Dalilin da EFCC ta saki Sanata Tambuwal
Jami'in EFCC ya ce:
“An riga an ba shi beli. Mun karɓi bayanan da muke buƙata daga gare shi, kuma nan ba da jimawa ba zai bar babban ofishinmu bayan kammala sharuddan belinsa.”

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
Da aka tambaye shi ko tsohon gwamnan zai fuskanci tuhuma ko a gurfanar da shi a kotu, jami'in na EFCC ya ki yarda ya yi karin bayani.
An kira mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ta wayar tarho sau da dama don samun bayani a hukumance game da lamarin, amma bai amsa ba.

Source: UGC
Bugu da kari, bai bayar da amsar saƙonnin da aka tura masa ba har zuwa lokacin da muka hada maku wannan rahoto.
Matakin EFCC na kama tsohon gwamna, Aminu Tambuwal ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin yan Najeriya, wasu na ganin siyasa ta sa aka kama shi saboda yana cikin hadakar yan adawa.
ADC ta nuna bacin ranta kan kama Tambuwal
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC da zama karen farautar gwamnatin tarayya domin tsoratar da kuma bata sunan shugabannin adawa.
ADC ta yi wannan zargin ne yayin da take martani kan tsare tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da hukumar EFCC ta yi.
Mai magana da yawun ADC ya yi ikirarin cewa EFCC na kama yan adawa da muzguna masu yayin da yan APC kuma ke yadda suke so ba tare da an masu komai ba.
Asali: Legit.ng
