Tsare Tambuwal Ya Fusata Jam'iyyar ADC, Ta Fayyace Shirin Hukumar EFCC
- Jam'iyyar ADC ta fito ta yi magana kan matakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta dauka na tsare Aminu Waziri Tambuwal
- Kakakin ADC ya bayyana cewa hukumar EFCC ta koma karen farautar jam'iyyar ADC don muzgunawa 'yan adawa
- Bolaji Abdullahi ya nuna cewa EFCC na muzgunawa 'yan adawa yayin da take kawar da kai ga mutanen da ke cikin jam'iyyar APC mai mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi martani kan kamun da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta yi wa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Jam'iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC da zama karen farautar gwamnatin tarayya domin tsoratar da kuma bata sunan shugabannin adawa.

Source: Twitter
Mukaddashin sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta zargi EFCC da nuna son kai
Bolaji Abdullahi ya yi zargin cewa hukumar EFCC ta fara shirin yi wa 'yan adawa dauki dai-dai.
Sakataren yada labaran ya ce tsare Aminu Waziri Tambuwal, da kuma “gaggawar” EFCC wajen neman bayanai kan mulkin watanni bakwai na tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, duk suna da alamar siyasa.
Kakakin na ADC ya kuma soki yunkurin hukumar na binciken tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, wanda shi ne mai rikon mukamin shugaban ADC na kasa, kan lokacin da ya jagoranci majalisar.
"ADC, kamar dukkan 'yan Najeriya, na nuna alamar tambaya kan lokaci, nuna wariya kan wadanda za a kama da kuma son zuciyar siyasa da ke bayyana a ayyukan EFCC."
“Yaki da cin hancin da ya tsaya kawai ga bangaren adawa ba adalci ba ne, zalunci ne. Babu shakka wannan farauta ce, gwamnatin APC tana amfani da yaki da cin hanci a matsayin makami na siyasa."

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
- Bolaji Abdullahi
ADC ta ce EFCC na son nakasa 'yan adawa
Bolaji Abdullahi ya ce binciken EFCC kan shugabannin adawa na da nufin rage musu karfin gwiwa kafin zaben 2027.
“Da zarar tsohon gwamna ya koma jam’iyya mai mulki, fayil dinsa na bacewa kamar hazon da ya bayyana da safe."
“Tun da Ifeanyi Okowa ya shiga APC, shin ’yan Najeriya sun taba jin EFCC ta sake magana kan batunsa?"
"Amma kuwa shugabannin adawa ana gallaza musu da zarge-zargen shekaru da dama da suka gabata ba tare da wata sabuwar hujja ba."
- Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ki yarda da abin da ya kira amfani da hukumomin gwamnati wajen cimma manufar siyasa.
“Yau David Mark ne, Ihedioha da Tambuwal. Gobe, zai iya zama duk wanda ya yi kokarin tabbatar da cewa wannan gwamnati ta yi abin da ya dace."
- Bolaji Abdullahi
Sule Lamido ya gano kuskure a ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana kuskuren da 'yan hadaka suke yi a ADC.
Sule Lamido ya bayyana cewa da yawa daga cikin 'yan hadakar suna gaggawar fitowa su nuna yunwarsu kan tsayawa takara.
Tsohon gwamnan ya bukace su da su tsaya gina tsari mai kyau wanda zai sanya su iya raba jam'iyyar APC da mulki a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

