Shugabar FCC Tana Murnar Tinubu Ya Tsawaita Wa'adinta, An Sanar da Korar ta daga Ofis
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi amai ya lashe game da sabunta nadin Muheeba Dankaka a matsayin shugabar hukumar FCC
- Kasa da awanni hudu bayan sabunta nadin Muheeba, Bola Tinubu ya sauke ta sannan ya maye gurbin da tsohuwar yar Majalisa, Ayo Hulayat Omidiran
- Wannan lamari dai ya haifar da rudani, har Mai Martaba Sarkin Ilorin ya taya Muheeba murna ba tare da sanin Tinubu ya sauya ra'ayi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - A ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025, shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi nadi mai cike da rudani a hukumar FCC ta kasa.
Tinubu ya sabunta nadin Muheeba Dankaka a matsayin shugabar hukumar FCC da misalin ƙarfe 6:35 na yamma, sai kuma ya sauke ta ya naɗa tsohuwar ‘yar majalisa, Ayo Hulayat Omidiran, a ƙarfe 10:44 na dare.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Sanatan da ke shirin neman takarar shugaban kasa ya rasu a Colombia

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da duka nade-nadin biyu a shafinsa na X, amma daga baya ya goge sanarwar tsawaita wa'adin Muheeba Dankaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan naɗi da sokewa mai ban mamaki ya haifar da ruɗani a ƙasar, inda wasu manyan mutane, ciki har da Sarkin Ilorin, suka taya Muheeba Dankaka murna bisa “sake naɗinta” duk da cewa Tinubu ya janye wannan naɗi.
Yadda Tinubu ya yi nadi kuma ya soke a FCC
A cikin sanarwar farko, fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu ya amince da sake nada Muheeba, tare da naɗin Mohammed Musa a matsayin sakataren hukumar FCC da kuma cikakken jerin sunayen kwamishinoni na jihohi.
Kayode Oladele daga jihar Ogun ya ci gaba a matsayin kwamishina bayan ya yi aikin shugabam riko tun bayan ƙarewar wa’adin farko na Muheeba Dankaka.
Amma bayan ƙasa da sa’o’i huɗu, fadar shugaban ƙasa ta sake fitar da wata sanarwa wacce ta ce “ta fi wadda aka fitar a baya ƙarfi,” inda ta ayyana Omidiran a matsayin sabuwar shugabar FCC.
Tinubu ya soke madin Muheeba Dankaka
Wannan sauyin ya kawo ƙarshen wa’adin Muheeba Dankaka wacce ake ganin wa'adinta na farko cike yake da takaddama da rikice-rikice a hukumar
Jerin sabbin naɗe-naɗen ya kasance kusan iri ɗaya, sai dai an ƙara Abdulwasiu Kayode Bawalla a matsayin kwamishinan FCC na jihar Legas.
Omidiran, tsohuwar ‘yar majalisar wakilai daga jihar Osun, yanzu ce za ta jagoranci hukumar wacce ke da alhakin tabbatar da adalci a rabon mukamai da albarkatun tarayya.

Asali: Twitter
An jefa Sarkin Ilorin a wannan rudani
Da safiyar Talata, ba tare da sanin wannan sauyi ba, Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, ya yi godiya ga Tinubu bisa sake naɗa Muheeba Dankaka, wacce take ɗaya daga cikin mutanensa.
Ya yaba mata kan “kyakkyawan aiki” da ta yi, tare da yi mata fatan nasara a sabon wa’adin da yanzu ya zama tarihi sakamakon sauyin ra’ayin Tinubu, rahoton Premium Times.
Wannan lamari ya shiga jerin kura-kuran naɗe-naɗen gwamnatin Tinubu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, inda aka sha janye ko gyara sanarwar naɗi.
Tinubu ya ba tsohon ciyaman a Kano mukami
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC).
Kafin wannan naɗin, Abdullahi Ramat ya rike mukamin shugaban ƙaramar hukumar Ungogo da ke Kano daga shekarar 2021 zuwa 2024.
Fadar shugaban kasa ta aanarda cewa wanda aka nada zai fara aiki ne a matsayin mukaddashin shugaba kafin Majalisar Tarayya ta tantance shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng