Gungun 'Yan Ta'adda Sun Kutsa Masallaci a Sakkwato, Sun Budewa Masallata Wuta

Gungun 'Yan Ta'adda Sun Kutsa Masallaci a Sakkwato, Sun Budewa Masallata Wuta

  • Jama'a sun dimauce a lokacin da wasu ‘yan bindiga sun kai hari a masallaci a ƙauyen Marnona, da ke jihar Sakkwato
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun dura a masallacin da Asuba, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi
  • Ana zargi maharan sun fito daga sansanonin ‘yan bindiga a dazuzzukan Sakkwato da Zamfara domin kawo harin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – An sake samun tashin hankali a jihar Sakkwato bayan wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kan masallata a ƙauyen Marnona, karamar hukumar Wurno.

Lamarin, da ya faru yayin sallar asuba, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu, abin da ya ƙara tsananta fargaba a yankin Sakkwato ta Gabas da ke fama da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Mutane sun yi takansu': Halin da ake ciki a Borno bayan Boko Haram ta kashe sojoji

'Yan ta'adda sun damu mazauna Sakkwato
'Yan ta'adda sun kai hari masallaci a Sakkwato Hoto: Leit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ganau sun bayyana yadda maharan, dauke da makamai masu yawa, suka kutsa cikin masallacin da sassafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani kuma suka fara harbi ba kakkautawa, lamarin da ya girgiza al’umma, inda mazauna yankin su ka tsere domin tsira da rai.

APC ta yi magana kan harin Sakkwato

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sakkwato, Hon. Isah Sadeeq Achida, ya yi Allah-wadai da lamarin, wanda ya bayyana da aiki na rashin imani da kuma rashin kunya.

Ya ce:

“Dole a kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan hari, kuma dole mu kasance tsintsiya madaurinki ɗaya wajen shawo kan wannan annoba.”

Achida ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin jiha tare da jami’an tsaro na aiki tuƙuru domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a Sakkwato da kewaye.

Ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu

Yadda aka kai harin Sakkwato

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kila maharan sun fito daga sansanonin da ke cikin dazuzzukan da suka haɗa jihohin Sakkwato da Zamfara, waɗanda aka sani da zama mafaka ga ‘yan bindiga.

An ruwaito cewa maharan sun tsere kafin isowar jami’an tsaro domin gudun fafata wa da jami'an da su ka kawo dauki.

Wannan harin ya ƙara yawan jerin munanan hare-haren da ake samu a yankin Sakkwato ta Gabas, wanda ya shafe watanni yana fama da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma kisan gilla.

Sojojin Najeriya sun kai dauki Sakkwato
Jama'a sun ce yan ta'adda sun tsere kafin isar sojoji Sakkwato Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Getty Images

Mazauna yankin sun yi ta kira ga hukumomi da su ƙara yawan sojoji tare da ƙarfafa haɗin kai wajen dawo da zaman lafiya.

Hukumomi sun shawarci jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da hanzarta sanar da duk wata motsi da ake zargin na bata gari ne ga jami’an tsaro.

'Yan ta'adda sun kori jama'a a Sakkwato

A wani labarin, kun ji cewa hain 'yan ta'adda ya tsananta a Tureta da Dange/Shun a jihar Sakkwato lamarin da ya jawo mazauna yankin su ka fara neman mafaka.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

Kauyukan da su ka shahara a wajen a yanzu sun zama kufai, bayan mazauna sun tsere saboda tsoro da yawaitar hare-haren ba tare da an samu daukin da ake bukata ba.

Hare-haren ‘yan bindiga sun jawo dubunnan mazauna yankunan suna ƙaura da zama 'yan gudun hijira, yayin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng