Nasara daga Allah: Sojoji Sun Babbake Yan Bindiga Fiye da 100 a Zamfara, an Yada Hotuna
- Sojojin Najeriya sun gano gawarwakin yan bindiga fiye da 60 bayan luguden wuta kansu a Zamfara da ake kukan rashin tsaro
- Sama da babura 30 da makamai sun kone, fiye da ‘yan ta’adda 100 sun mutu a harin da aka kai wanda ya kara rikita yan ta'addan
- Rundunar ta ci gaba da farautar maboyarsu domin hana sake haduwa ko kai hari a cikin dazukan yankin da ke fama da matsalolin tsaro
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Yan bindiga da dama sun bakunci lahira bayan wani hari da sojoji suka kai musu a jihar Zamfara.
Sojojin Najeriya sun gano gawarwakin yan bindiga fiye da 60 da ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar bayan luguden wuta na rundunar sojin saman Najeriya.

Source: Facebook
Sojojin sama sun babbake 'yan bindiga a Zamfara
Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa an gano gawarwakin ne a kauyen Matseri na karamar hukumar Anka da sojojin suka kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin ya biyo bayan bayanan leken asiri, inda rundunar sojin sama ta kai luguden wuta kan sansanin ‘yan bindiga a ranar Lahadi 10 ga watan Agustan 2025.
An kai harin ne kan taron ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton za su kai farmaki a Nasarawan Burkullu na karamar hukumar Bukuyum a jihar Zamfara.

Source: Original
Gawarwakin 'yan bindiga nawa aka samu?
Bayan bincike, an gano gawarwaki yan bindiga sama da 60 da sassan jikinsu suka kone kurmus a wuraren da aka kai hari wanda ke kara tabbatar da nasarar sojoji.
Haka kuma an gano babura sama da 30 da makamai da dama sun kone kurmus a harin na sama da rundunar sojoji suka kai.
Majiyoyi sun nuna cewa luguden wutan ya shafi ‘yan ta’adda fiye da 400 ciki har da manyansu da dama a dajin Makakkari.
A jimlace, sama da ‘yan ta’adda 100 aka kashe, yayin da da dama suka tsere da raunuka.
Matsalar da harin ya jawowa 'yan bindiga
An bayyana cewa wannan farmaki ya karya karfin ‘yan bindiga da kuma hana kai harin ramuwar gayya da mafi yawan lokuta suke yi kan al'umma.
Rundunar ta dakile kokarin ‘yan ta’addan dawowa wajen daukar gawarwakin abokan su ta hanyar harba musu manyan bindigogi.
Sojoji sun ci gaba da sintiri da tsabtace wuraren domin hana ‘yan ta’addan sake taruwa ko kafa sabon sansani.
'Yan sanda sun dakile harin yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar dakile wani mugun nufi da 'yan bindiga suka shirya a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
Rundunar dai ta samu nasarar ne bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga sun tare wasu matafiya da ke kan hanyar Funtua zuwa Gusau domin yin ta'asa a yankin.
Bayan an yi artabu tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindiga, an samu nasarar kubutar da mutanen da aka yi yunkurin yin garkuwa da su wanda ya kwantarwa al'ummar yankin hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

