'Mun Yi Rashi': Aminu Ado Ya Kadu bayan Mutuwar Ministoci 2 a Hatsarin Jirgi

'Mun Yi Rashi': Aminu Ado Ya Kadu bayan Mutuwar Ministoci 2 a Hatsarin Jirgi

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya jajanta wa kasar Ghana kan rasuwar mutane takwas a hadarin jirgin sojojin kasar
  • A wani jawabi na musamman, ya bayyana lamarin a matsayin rashi ga Ghana, Najeriya da daukacin kasashen Yammacin Afirka baki daya
  • Basaraken ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan tare da bai wa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi da aka yi a nahiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi ta'aziyya kan rashin da kasar Ghana ta yi na jami'an gwamnati.

Basaraken ya bayyana ta’aziyya mai rasa zuciya ga gwamnatin Ghana, iyalan wadanda abin ya shafa, da al’ummar kasar.

Aminu Ado ya mikasakon ta'aziyya bayan hatsarin jirgi a Ghana
Aminu Ado ya ji ba dadi da aka samu hatsarin jirgin sama a Ghana. Hoto: Masarautar Kano.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Masarautar Kano ta yada a shafin X a jiya Litinin 11 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Sanatan da ke shirin neman takarar shugaban kasa ya rasu a Colombia

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka rasa manyan jam'an gwamnatin Ghana

Hakan ya biyo bayan rasuwar mutane takwas a hadarin jirgin sojoji da ya faru a Ghana wanda ya ta da hankulan mutanen kasar.

A ranar Laraba da ta gabata ne aka samu mummunan hatsarin jirgin sama a yankin Ashanti da ke kasar Ghana mai makwabtaka da Najeriya.

Ministan tsaro da na muhalli a ƙasar Ghana sun mutu tare da wasu mutum shida a hatsarin wanda ya sanya jimami a zukatan mutanen kasar.

Sojojin Ghana sun ce jirgin Z9 na daga birnin Accra zuwa Obuasi ya bace daga sama, inda yake dauke da mutane takwas ciki har da mukarraban gwamnati.

Rashin ministoci a Ghana ya taba Aminu Ado Bayero
Amino Ado Bayero ya tura sakon ta'aziyya ga gwamnatin Ghana kan rashin ministoci. Hoto: Masarautar Kano.
Source: Twitter

Sakon ta'aziyya daga Aminu Ado zuwa Ghana

An fitar da sanarwar a madadin masarautar Kano da al’ummar Kano, Sarkin ya ce wannan babban rashi ne ba wai ga Ghana kawai ba, har ma da Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Ina mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin Ghana, iyalai da dukkan al’ummar Ghana kan rasuwar mutanen da hadarin jirgin sojoji ya shafa.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu

“Lallai, wannan ba rashi ne na kasar Ghana kadai ba, har ma na mu ‘yan Najeriya, ‘yan’uwanku da ‘yan’uwanku a Yammacin Afirka.”

Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu sanadin hatsarin jirgin, tare da rokon Ubangiji ya bai wa iyalansu da kasar Ghana hakurin rfin jure wannan babban rashi.

Wannan hadari ya samu ta’aziyya daga wurare daban-daban a yankin, inda kasashen Yammacin Afirka ke nuna goyon baya da nuna goyon baya a irin wannan mawuyacin lokaci.

“Allah ya sa sun huta, kuma ya ba mu hakurin daukar wannan babban rashi a zukatanmu."

- Cewar sanarwar

Mutuwar ministoci: Tinubu ya jajantawa kasar Ghana

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa takwaransa na ƙasar Ghana, John Dramani Mahama bisa rasuwar ministocinsa biyu da wasu mutum shida.

Ministan tsaron Ghana da ministan Muhalli da sauran mutane har guda shida na cikin wadanda suka rasa ransu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Bola Tinubu ya yi alhinin wannan hatsari tare da mika sakon ta'aziyya a madadin gwamnatin Najeriya ga ƴan uwa da abokan arziki na ƙasar Ghana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.