Abubuwan da Za a Duba kafin Kirkiro Sababbin Jihohi a Kano da Wasu Sassan Najeriya
- Yan Najeriya daga sassa daban-daban sun mika bukatun kirkiro sababbin jihohi a tarukan sauraron ra'ayoyin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulki
- Kano da sauran jihohin Arewa maso Yamma na cikin wadanda suka nemi karin jihohi saboda yawan jama'a da albarkacin fadin kasa da suke da shi
- Majalisar Dattawa ta bayyana cewa za ta duba ka'idoji da duka abubuwan da doka ta tanada kafin amincewa da kirkiro ko wace jiha da aka bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Dattawa ta bayyana cewa za ta yi la’akari da dukkan muhimman abubuwa da suka wajaba kafin ta amince da bukatum ƙirƙiro jihohi a Najeriya.
Majalisar ta ce za ta yi amfani da duka ka'idoji da sharuddan da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada kafin ta amince a samar da karin jihohi a kasar nan.

Source: Facebook
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana haka a yayin da yake hira da Nigerian Tribune a garinsa na Ilawe-Ekiti, Jihar Ekiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta yi magana kan kirkiro jihohi
Ya ce duk da yan Najeriya na ci gaba da kiraye-kirayen kirkiro jihohi, za a gudanar da lamarin cikin gaskiya, ba tare da nuna son zuciya ba.
Idan baku manta ba, masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban ciki har da Kano sun mika bukatar kirkiro jihohi a taron sauraron ra'ayoyin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulki.
Da yake larin haske kan lamarin, Sanata Adaramodu ya cewa zuwa yanzu, Majalisar Dattawa ta karbi bukatu akalla 61 kan batun kirkiro sababbin jihohi.
Sanatan da ke wakiltar Ekiti ta Kudu ya tabbatar da cewa za a bi doka da ka’ida yadda ya kamata kafin amincewa da kowace bukata.
Abubuwan da za a duba wajen kirkiro jihohi
A rahoton The Cable, Yemi Adaramodu ya ce:
“Zuwa yanzu, Majalisar Dattawa ta karɓi buƙatu kusan 61 na ƙirƙirar jihohi a tarukan da muka yi da ‘yan ƙasa daga dukkanin shiyyoyi guda shida na kasar nan.
"Za mu tattara su, sannan Kwamitin gyaran Kundin Tsarin Mulki ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, zai haɗa su ya yi nazari, da tace su kafin ya shirya rahotonsa.
“Da zarar an gama rahoton, Majalisar Dattawa tare da Majalisar Wakilai za su yi zaman jin ra’ayin jama’a. Wannan zai bai wa dukkan masu ruwa da tsaki damar gabatar da hujjoji. Bayan haka, majalisun biyu za su yanke hukunci."

Source: Twitter
'Kirkiro sababbin jihohi abu ne mai girma'
Ya ƙara da cewa kirkirar jiha lamari ne mai muhimmanci da ke buƙatar bincike da nazari kan bayanan yawan jama’a, yanayin ƙasa, da tarihin yankin.
Ya ce a wasu lokuta ma, a cikin jihohin da suke neman a raba su, ba kowa ke goyon baya ba.

Kara karanta wannan
Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi
"Dukkan waɗannan abubuwa za mu yi la’akari da su. Har zuwa lokacin da za a kammala wannan matakai, Majalisar Tarayya ba za ta ba da shawarar ƙirƙirar jiha ko daya ba," in ji shi.
Da gaske Shugaban Majalisar Dattawa bai da lafiya?
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Gbenga Daniel ya karyata wannan jita-jitar da ake yadawa cewa an kwantar da shugaban Majalisar Dattawa a asibiti a Landan.
Sanatan mai wakiltar Ogun ta Gabas a inuwar APC, ya ce labarin da wasu kafafen watsa labarai ke yadawa ba gaskiya ba ne.
Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun ya fadi haka ne bayan ya kai wa Sanata Akpabio ziyara a birnin Landan na kasar Burtaniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

