An Kwantar da Shugaban Majalisar Dattawa a Wani Asibiti a Landan? An Samu Bayanai

An Kwantar da Shugaban Majalisar Dattawa a Wani Asibiti a Landan? An Samu Bayanai

  • Wasu rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa an kwantar da shugaban Majalisar Dattawa a wani asibitin Landan
  • Sanata Gbenga Daniel mai wakiltar Ogun ta Gabas ya ziyarci shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a birnin Landan domin gano gaskiya
  • Daniel, wanda tsohon gwamnan jihar Ogun ne ya bayyana cewa labaran da ake yadawa cewa Akpabio ba shi da lafiya ba gaskiya ba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - An fara rade-radin cewa shugababan Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio na kwance ba shi da lafiya a wani asibiti da ba a bayyana ba a Landan.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Rundunar Sojin Ruwa, Sanata Gbenga Daniel ya karyata wannan jita-jita, ya ce Akpabio na cikin koshin lafiya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Labarin rashin lafiyar shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ba gaskiya ba ne Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Sanatan mai wakiltar Ogun ta Gabas a inuwar APC, ya ce labarin da wasu kafafen watsa labarai ke yadawa ba gaskiya ba ne, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata Amaechi kan batun hada kai da 'yan adawa a kawo ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Gbenga Daniel ya gana da Akpabio

Daniel ya bayyana cewa ya tsaya a Landan don ya sanar da Shugaban Majalisar Dattawa game da shirin komawarsa Najeriya domin halartar zaɓen cike gurbin da za a yi a watan Agusta, 2025.

A ranar 16 ga Agusta, 2025, INEC ta shirya gudanar da zaben dan Majalisar Wakilai a mazabar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa a Ogun, domin maye gurbin Hon. Adewumi Onanuga, wanda ya rasu.

Da yaje jawabi yayin ganawa da Akpabio a Landan, Sanata Daniel ya ce:

“Na zo ne na sanar da Shugaban Majalisar Dattawa, cewa zan koma Najeriya domin halartar zaɓen cike gurbi na 16 ga Agusta, 2025 a mazabar dan Majalisar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa.
"Kujerar dan Majalisar Wakilai ta zama babu kowa a kanta bayan rasuwar Hon. Onanuga. Ranka ya dade, labarin da ake yadawa shi ne ba ka da lafiya, amma abin da na gani daban, na ji dadin haka.

Kara karanta wannan

2027: 'Dan majalisa ya yi hasashe kan yiwuwar takara tsakanin Tinubu da Jonathan

"Kujerar dan Majalisar Wakilai ta zama babu kowa a kanta bayan rasuwar marigayiya Hon. Onanuga. Ranka ya dade, labarin da ake yadawa shi ne ba ka da lafiya,

Da gaske Shugaban Majalisar Dattawa bai da lafiya?

A cikin wata sanarwa da kakakin Akpabio, Jackson Udom, ya fitar, ya ce shugaban Majalisar Dattawa ya gode wa Sanatan Ogun bisa ziyarar da ya kai masa, inji Daily Post.

Akpabio ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa, bisa bayanan da yake da su, jam’iyyar APC za ta lashe zaɓen cike gurbin da za a yi a jihar Ogun.

“Tare da goyon bayan Gwamna Dapo Abiodun, kai da sauran shugabannin jam’iyyarmu a jihar Ogun, za ku tabbatar da nasarar APC a wannan mazaba," in ji shi.
Sanata Godswill Akpabio.
Akpabio ya ce idan aka daka ta kafafen sada zumunta, sai yaki ya barke Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Dangane da batun rashin lafiyarsa da ake yadawa, Akpabio ya ce, “Labaran kafafen sada zumunta za su iya tayar da yaki idan aka daka ta tasu."

Shin Shugaba Tinubu ba shi da lafiya?

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta musanta rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da lafiya.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Legas zai bar tafiyar Tinubu ya koma ADC? Ambode ya fayyace gaskiya

An fara yada wannan jita-jita ne sakamakon rashin ganin shugaban kasar a bainar jama'a na tsawon kwanaki duk kuwa da yana nan a gida Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce rahotanni da ake yadawa ba gaskiya ba ne, Tinubu na gudanar da aikinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262