Ajali Ya Gitta: Mata da Miji da Wasu Mutum 3 Sun Rasu Lokaci Guda a Katsina

Ajali Ya Gitta: Mata da Miji da Wasu Mutum 3 Sun Rasu Lokaci Guda a Katsina

  • Mazauna unguwar Abattoir a jihar Katsina sun shiga jimami sakamakon wani mummunan hatsari da ya rutsa da wasu ma'aurata
  • Ma'auratan sun rasa rayukansu ne a titin Kurfi zuwa Katsina yayin dawowa daga duba wata mara lafiya
  • Wani mazaunin unguwar ya tabbatarwa Legit Hausa cewa magidancin mai suna Abdulsalam Yusuf, mutumin kirki ne kuma yana cikin limamansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - An shiga tashin hankali da jimami a unguwar Abattoir da ke cikin birnin Katsina sakamakon mutuwar wasu ma'aurata da ba su jima da aure ba.

Ma'auratan sun rasa rayukansu tare da wasu mutum uku a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a titin Kurfi zuwa Katsina.

Marigayi AbdulSalam da matarsa.
Hatsarin mota ya yi ajalin mata da miji a Katsina Hoto: Abubakar Rabiu Dabai
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa ma'auratan da suka rasu a hatsarin su ne, Abdulsalam Yusuf Kankara, mai shekara 37, da matarsa Malama Zainab.

Kara karanta wannan

Jama'a sun 'dimauce da tankokin mai su ka fashe a Zariya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mata da miji suka rasu a Katsina

An ruwaito cewa lamarin ya auku lokacin da mata da mijin suka kamo hanyar dawowa bayan sun je duba wata mata da ta yi 'bari a karamar hukumar Kurfi.

Ɗan’uwan Marigayi Abdulsalami, Aminu Yusuf Kankara, ya ce wani babur da ya ɗauko mutane uku ne ya yi karo da motarsu, lamarin da ya zama ajalinsu.

“Duka mutane uku da ke kan babur ɗin da matar Abdulsalam sun rasu nan take a wurin amma shi Abdulsalami, daga baya ya rasu a asibiti,” in ji shi.

Abin da ya haddasa faruwar hatsarin

Wasu ganau da abin da ya faru a kan idonsu sun shaida wa manema labarai cewa mai babur ɗin, wanda ke ɗauke da fasinjoji biyu, ne ya fadawa motar ma'auratan.

A cewarsu, duka mutanen da ke kan babur din da mutum daya daga cikin wadanda ake cikin motar sun mutu nan take a wurin da hatsarin ya afku.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

Ganau sun kara da cewa sauran mutane uku da ke cikin motar an garzaya da su asibiti, inda daga baya Abdulsalami ya riga mu gidan gaskiya sakamakon raunukan da ya samu.

Hatsari ya lakume rayukan mutum 5 a Katsina.
Mazauna unguwar Abbatoir a Katsina sun yi rashin daya daga cikin limamansu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda Abdulsalam ya yi bankwana da mutane

Wani malamin jinya, Nas Abubakar Rabiu Dabai ya tabbatar da wannan lamari ga Legit Hausa, inda ya bayyana cewa Abdulsalam ya yi aure ne bara.

Abubakar ya ce:

"Sun rasu ne a mummunan hatsarin mota jiya a hanyarsu ta dawowa daga Kurfi, Abdulsalam abokinmu ne a Katsina, muna zaune a unguwa daya.
"Muna zama a majalisa daya da shi, mutum ne mai saukin kai kuma mai kirki, shi ke mana limancin sallah. Shi ya ja sallah ta Azahar ranar Asabar, ya yi ladanci a sallar La'asar wanda yayi limanci ya yi wa'azi a kan mutuwa.
"Bayan sallah ya ce za su je Kurfi tare da iyalinshi don gaida mara lafiya. A hanyarsu ta dawo wa suka yi hatsari rai yayi halinsa."

Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 22

A wani labarin, kun ji cewa akalla mutane 22 aka tabbatar da mutuwarsu a wani mummunan hatsarin tirela da ya auku a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Wasu na kiran sulhu, ƴan bindiga sun hallaka malamin addini da wasu mutane

Tirelar na dauke da mutane da dabbobi daga Kano zuwa Legas lokacin da ta yi hatsari da karfe 3:00 na daren Litinin a titin Lambata.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja ta sanar da cewa mutane 20 da suka tsira a hatsarin, sun samu munanan raunuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262