Kano: Abin da Hadimin Abba Ya ce bayan Korarsa saboda Zargin Hannu a Belin Dilan 'Kwaya

Kano: Abin da Hadimin Abba Ya ce bayan Korarsa saboda Zargin Hannu a Belin Dilan 'Kwaya

  • Abubakar Umar Sharada, tsohon mai ba gwamna Abba Kabir Yusuf da aka kora ya magantu a kan raba shi da kujerarsa a jihar Kano
  • Gwamnatin Kano ta sanar da korar Abubakar a ranar Asabar bayan binciken wani kwamiti ya alakanta shi da Suleiman Ɗanwawu
  • Ana zargin Abubakar yana da hannu a yadda aka shiga aka fita domin karbo belin Ɗanwawu da ake zargi da dillancin kwaya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Abubakar Umar Sharada, tsohon hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi martani kan raba shi da mukaminsa a Kano.

Abubakar Sharada shi ne tsohon mai ba da shawara ta musamman kan wayar da kan jama’a game da siyasa ga Gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Danwawu: Abba ya fatattaki hadimi a Kano saboda hannu a belin dilan kwaya

Gwamna Abba Kabir Yusuf da Abubakar Umar Sharada
Tsohon hadimin Abba ya yi magana kan korarsa Hoto: Abba Kabir Yusuf/Abubakar Umar Sharada
Asali: Facebook

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana abin da a ganinsa ya jawo masa kora daga gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnatin Abba na korar Abubakar Sharada

A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnatin Kano ta fitar da sanarwa cewa ta kori wasu hadiman gwamna Abba Kabir Yusuf bisa dalilai daban-daban.

Abubakar Umar Sharada ya rasa kujerarsa ne bayan binciken kwamitin gwamnatin Kano kan zargin belin dilan ƙwaya, Suleiman Ɗanwawu.

Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano, Abba Kabir Yusuf faɗi dalilin korar Abubakar Umar Sharada Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta lamunci wasu daga cikin jami’anta suna aikata ayyukan da ba su dace ba, wadanda ka iya kawo cikas ga ci gaban Kano.

Martanin tsohon hadimin gwamnan Kano

A martaninsa, Abubakar Umar Sharada ya kwantar wa da magoya bayansa hankali game da matakin korar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka a kansa.

A kalamansa, ya ce:

"Innalillahi innalillahi innalillahi. Alhamdulillah Allah mun gode da ni’imarKa a garemu muna godiya."

Kara karanta wannan

Kungiyar gwamnoni ta zabi gwamna 1 da ya fi kowa kokari a 2025

"Masoya kowa ya kwantar da hankalinsa, ba komai."
"Insha Allah zai zama alheri Insha Allah."
"Soyayya ce ta ja mana kuma bakomai, ta mu ta yi kyau."

Martanin jama'a ga tsohon hadimin Abba

Jama'a da dama sun yi martani ga sakon da Abubakar Umar Sharada ya wallafa, inda wasu ke masa addu'ar Allah Ya musanya masa da mafi alheri.

Khatimu Kabir Umar ya ce:

Nan fa aka zo ana maganar belin dilan kwaya, ka rika nuna hakan ba wani abu ba ne. karshe gaskiya ta yi halinta kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi gaba da kujerarku. mu dai sai mu ce Allah Yasa hakan ya zama izina gare ka da mu da 'yan baya baki ɗaya."

Isah Suleiman Ibrahim ya ce:

"Allah ya musanya da Alheri."

Gwamnan Kano ya kori hadimansa 2

A baya, kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta tabbatar da korar manyan hadimai biyu na musamman (SSAs).

Kara karanta wannan

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne bayan samun rahoton kwamitoci na musamman da suka alakanta su da aikata ayyukan da ba su dace ba.

A cewar rahoton, an samu ɗaya daga cikin hadiman da shiga harkar belin dilan ƙwaya, Sulaiman Aminu Danwawu, ɗayan kuma ya karkatar da tallafi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.