Sarakunan Gargajiya daga Ketare Sun Shiga Fadar Sanusi II, Sun Yi Masa Mubaya'a
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu mubaya'a daga manyan sarakunan gargajiya daga Jamhuriyar Nijar da jihar Yobe
- Sarakunan daga Yobe sun hada da Sarkin Machina Alhaji Bashir Albishir Bukar da Mai Jajere Alhaji Hamza Buba Mashigo
- Daga Nijar kuwa akwai Abdu Kachalla Gasa Maine Dipa, Bubakar Yahaiya Lushe Bande, Abubakar Marafa Kyasa Tsibiri da Hassan Musa Angu Baraguine
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na ci gaba da samun goyon baya daga manya da kuma sarakunan gargajiya.
Wasu sarakunan gargajiya daga ketare ma sun shiga har fadar basaraken a kano inda suka nuna goyon bayansu gare shi.

Source: Twitter
Manyan sarakuna sun yiwa Sanusi II mubaya'a
Shafin Sanusi II Dynasty ne ya tabbatar da haka a yammacin yau Lahadi 10 ga watan Agustan 2025 a manhajar Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce manyan sarakunan gargajiya daga Jamhuriyar Nijar da dama sun yi mubaya'a ga Sarki Sanusi II a Kano.
Har ila daga cikin wadanda suka yi mubaya'ar akwai sarakunan gargajia daga jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sarakunan daga sun hada na Machina, Alhaji Bashir Albishir Bukar, da Mai Martaba Mai Jajere, Alhaji Hamza Buba Mashigo.
Sanarwar ta ce:
"Masu martaba sarakunan gargajiya a Jamhuriyar Nijar da na Jihar Yobe sun kai ziyarar mubaya’a ga Mai Martaba Sarkin Kano.
"Sarakunan sun ziyarci Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, a fadar sa da yammacin yau, Lahadi 10 ga watan Agustan 2025.
"Wadanda suka halarta daga Jihar Yobe sun haɗa da Mai Martaba Sarkin Machina, Alhaji Bashir Albishir Bukar, da Mai Martaba Mai Jajere, Alhaji Hamza Buba Mashigo."

Source: Facebook
Sarakunan da suka ziyarci Sanusi II
Har ila yau, an jero sarakunan da suka kai ziyara fadar Sarki Sanusi II daga Jamhuriyar Nijar domin nuna masa mubaya'a.
An lissafo sarakunan gargajiyan kamar haka, Mai Martaba Abdu Kachalla Gasa Maine Dipa, Mai Martaba Bubakar Yahaiya Lushe Bande na Zinder.
Sannan akwai Mai Martaba Abubakar Marafa Kyasa Tsibiri na Dosso, Mai Martaba Hassan Musa Angu Baraguine na Zinder.
Majiyoyi sun kuma tabbatar da cewa a cikin masu ziyarar akwai mai ba shugaban Nijar shawara, Bubakar Hassan.
"Daga Jamhuriyar Nijar kuma sun haɗa da Mai Martaba Abdu Kachalla Gasa Maine Dipa, Mai Martaba Bubakar Yahaiya Lushe Bande na Zinder.
"Sai kuma Mai Martaba Abubakar Marafa Kyasa Tsibiri na Dosso, Mai Martaba Hassan Musa Angu Baraguine na Zinder, tare da Bubakar Hassan, mai ba wa shugaban ƙasar Nijar shawara."
- Cewar Sanarwar
Sarkin Kofa ya yi mubaya'a ga Sanusi II
Kun ji cewa Balarabe Sarkin Kofa ya tuba a gaban Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II saboda rashin biyayya da ya nuna a baya.
Rahotanni sun nuna cewa a gaban manyan 'yan fada ya furta kalmomin tuba tare da yin mubaya’a ga Mai Martaba Sarkin.
Ya janye goyon bayansa ga fadar Nasarawa, ya kuma bukaci afuwa bisa goyon bayan da ya baiwa Aminu Ado Bayero a baya.
Asali: Legit.ng

