Rikici Ya Kaure tsakanin Dogo Gide da Hatsabibin Ɗan Bindiga, an Kashe Wasu
- Rikicin da ya barke tsakanin Dogo Gide da Kachalla Alti a Tsafe, Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da sace wasu shida
- Rahotanni sun ce maharan sun tilasta wa mazauna kauyuka aiki a gonar Dogo Gide, inda Kachalla Alti ya kai farmaki ya yi garkuwa
- Daga baya jami’an tsaro sun ceto wani da ya jikkata tare da samun gawarwaki biyu, yayin da aka saki fursunoni da yamma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Harin ’yan bindiga da aka kai kwanan nan a karamar hukumar Tsafe ta Zamfara ta rikita jama'a a jihar.
Wannan harin ya sake tabbatar da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma wanda ke ci gaba da tayar da hankulan al'umma.

Asali: Original
An rasa rayuka bayan rikicin yan bindiga
Majiyar tsaro ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Asabar 9 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa harin da ya faru ranar 9 ga watan Agusta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da sace wasu shida.
An ce hakan ya samo asali ne daga rikici tsakanin manyan ’yan bindiga Dogo Gide da Kachalla Alti.
Hakan ya faru ne lokacin da aka tilasta mazauna Keta, Kwaren Gabuwa da Bawa Ganga yin aiki a gonar Dogo Gide.
Yadda rigimar ta fara a Zamfara
Yayin da mutanen ke aiki a gonar da ke wajen Keta, wani jagoran ’yan bindiga, Kachalla Alti, ya kai hari mai ramuwar gayya inda ya sace mutane shida nan take.
Da yamma, da misalin ƙarfe 5:20, jami’an tsaro suka gano gawarwaki biyu tare da ceto wani mutum da ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
A cikin abin mamaki, an saki mutanen da aka sace da misalin ƙarfe 8:30 na dare, mai yiyuwa ne saboda tattaunawa ko yarjejeniya tsakanin kungiyoyin.
An kai gawarwakin da wanda ya jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Tsafe domin yin gwaji da kuma samun kulawar lafiya daga likitoci.

Asali: Twitter
Yan sa kai sun fara sintiri a Zamfara
A halin yanzu jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai sun kara yawan sintiri a yankin domin dakile sake faruwar irin wannan hari.
Dogo Gide na daga cikin manyan masu ta’addanci da ke da ikon manyan hanyoyin aikata laifi a Zamfara, Katsina, Neja da wasu sassan Kaduna.
An alakanta shi da garkuwa da mutane, kisan gillar mutane da dama, da kuma kai hare-hare kan jami’an tsaro da wuraren aiki a jihohin Arewa maso Yamma.
Yan bindiga sun hallaka junansu a Zamfara
Kun ji cewa tawagar 'yan bindiga biyu ma su hamayya da juna sun kaure da faɗa tsakaninsu kan yunkurin kwace ikon wani yankin Zamfara.
Lamarin ya faru ne a wani jejin karamar hukumar Maru, jihar Zamfara inda ‘yan ta’addan suka yi kaurin suna wajen farmakar jama'a.
Majiyoyin leken asiri sun shaida cewa akalla ‘yan ta’adda 16 suka mutu a arangamar, ciki har da wasu manyan jagorori guda biyu.
Asali: Legit.ng