An Kuma: Miyagu a Kudu Sun Raunata Direba daga Arewa, Sun Ƙona Motarsa

An Kuma: Miyagu a Kudu Sun Raunata Direba daga Arewa, Sun Ƙona Motarsa

  • Wasu matasa yan daba dauke da adduna sun kai wa direban mota daga yankin Arewacin Najeriya hari a Kudu maso Gabashin kasar
  • An raunata Dallami Yunusa yayin harin a kwanan Ogi da ke karamar hukumar Okigwe a Imo a yankin Kudu
  • Matasan sun jikkata shi sannan suka kona motarsa kamar yadda shugaban kungiyar direbobi ya fada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Okigwe, Imo - Wasu bata gari sun kai hari kan direban mota a ƙaramar hukumar Okigwe da ke jihar Imo.

Harin ya rutsa da wani matashi mai suna Dallami Yunusa a kwanan Ogi inda aka jikkata shi tare da kona motarsa.

Wasu miyagu sun raunata direba daga yankin Arewa
An kai wa direba daga Arewa hari a Imo. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Shugaban kungiyar NURTW, sashen manyan motoci a Okigwe, Dahiru Musa Raza, ya tabbatar da lamarin ga wakilin Daily Trust.

Yadda ake kisan yan Arewa a Kudancin Najeriya

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

Wannan ba shi ne karon farko da ake kai farmaki kan yan Arewa da ke Kudancin Najeriya musamman direbobi wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Ko a watan Yunin 2025, wasu ƴan bindiga sun kashe direbobi biyu tare da kona tirela a jihar Imo, kamar yadda hukumar NURTW ta tabbatar da lamarin.

Kungiyar NURTW ta zargi ƴan IPOB da kai harin, aka ce sun tare hanya tare da buɗe wuta kan direbobin, sannan suka kone gawarsu da motar.

Hon. Balarabe Danja ya yi kira ga kungiyar gwamnonin Arewa da ta dauki mataki kan irin asarar rayukan 'yan Arewa da ake yi a Kudu.

An kona motar yan Arewa a Imo
Mutane sun jikkata bayan raunata direba daga Arewa a Kudu. Hoto: Legit.
Source: Original

NURTW ta koka kan kona motar yan Arewa

Shugaban kungiyar NURTW, Raza ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne tun ranar Talata 5 ga watan Agustan shekarar 2025 da muke ciki.

Ya bayyana cewa motar direban ta samu matsala ne, kuma yayin gyara, wasu biyu dauke da adduna suka kai hari, sauran suka tsere, amma direban ya jikkata.

Raza ya ce suna ganin direban kamar ya mutu, sai suka kunna wuta suka kone motar sannan suka tsere, kafin sojoji su iso wurin.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

Yadda sojoji suka kawo dauki a Imo

Sojojin sun same shi da rai, suka garzaya da shi asibiti a Okigwe, daga nan aka mayar da shi asibitin Dala a Kano domin ci gaba da jinya.

Raza ya kara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda, sai dai kakakin rundunar jihar Imo, Henry Okoye, bai samu rahoto ba tukuna.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wata sanarwa daga rundunar yan sanda ko hikimomi kan kai hari kan Hausawa

An hallaka Hausawa a Plateau

Mun ba ku labarin cewa wasu matasa masu tayar da hankali sun kai hari kan fasinjoji a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau, inda suka kashe mutum tare da jikkata wasu 21.

Fasinjojin ‘yan kabilar Hausa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin aure a Qua’an-Pan, amma sun bace suka shiga wani yanki na karamar hukumar Mangu.

Cikin gaggawa, sojojin Najeriya karkashin Operation Lafiyan Jama’a suka kai dauki inda suka ceci rayuka da dama tare da kai wadanda suka jikkata asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.