Tsohon Gwamnan Legas Zai Bar Tafiyar Tinubu Ya Koma ADC? Ambode Ya Fayyace Gaskiya
- Akinwunmi Ambode ya karyata jita-jitar ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai cewa har yanzu yana tare da Shugaba Bola Tinubu
- Tsohon gwamnan na Legas ya ce jita-jitar da ake yadawa zai koma ADC ba gaskiya ba ce, kuma zai goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027
- Ambode ya bukaci mazauna jihar Legas da su yi watsi da labaran karya, su maida hankali kan ci gaban jihar da Najeriya baki daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Tsohon gwamnan jihar Legas, Mr. Akinwunmi Ambode ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa na cewar zai fice daga jam'iyyar APC.
Wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta sun yi zargin cewa Ambode zai fice daga APC ne domin ya shiga jam'iyyar hadaka ta ADC.

Source: Facebook
Tsohon gwamna ya aika sako ga Tinubu
Sai dai, jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya ce wadannan rahotanni da ake yadawa ba gaskiya ba ne, karya ce tsagoronta ta 'yan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani kan jita-jitar da ake yadawa ta bakin daraktan kungiyar goyon bayan Tinubu-Ambode, Seyi Bamigbade, tsohon gwamnan ya aika sako ga shugaban kasa.
Mr. Akinwunmi Ambode ya shaidawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa har yanzu yana tare da shi, kuma zai goyi bayan tazarcensa a 2027.
Tsohon gwamnan Legas na APC daram
Sanarwar shugaban kungiyar Tinubu-Ambode ta ce:
"Mun ci karo da wasu rahotanni na karya da ake yadawa a soshiyal midiya da ke ikirarin Mr. Akinwunmi Ambode, tsohon gwamnan Legas zai nemi takarar gwamna karkashin jam'iyyar ADC.
"To muna so mutane su sani wannan karyace tsagoronta ake yadawa, kuma wasu karnukan 'yan farauta ne suka dauki kwangilar yadata don tayar da zaune tsaye.
"Har yanzu Mr. Ambode na tare da shugaban kasa Bola Tinubu da jam'iyyar APC, kuma ya jaddada biyayyarsa gare shi, wacce ba za ta taba sauka ba."

Source: UGC
An ba mazauna Legas muhimmiyar shawara
Punch ta rahoto Bamigbade ya kuma dage cewa Ambode bai taba gudanar da taruka ko tattaunawa ko tunubar jam'iyyar ADC ko wata jam'iyyar siyasa game da kudurinsa na takara ba.
Ya kuma bukaci wadanda suka dauko kwangilar yada wannan labarin karyar da su nemi wata hanyar cin abinci ta halar maimakon dogewa a kan yada bayanan karya.
Yayin da ya nuna yakininsa game da dorewar ci gaban Najeriya a karkashin gwamnatin APC a Legas da kasa, Bamigbade ya ce:
"Muna bukatar mazauna jihar Legas da su yi watsi da wadannan labaran karya da ake yadawa, sannan su mayar da hankali kan batutuwan da za su kawo ci gaba ga jihar da kasa baki daya."
Ambode ya fadi alheran marigayi Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Akinwunmi Ambode, ya yi jimamin rasuwar Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai tsoron Allah.
Tsohon gwamna, Ambode ya ce Buhari ya mara wa Legas baya sosai, inda ya amince da manyan ayyuka kamar gyaran hanyar filin jirgin saman MMIA.
Ya roki Ubangiji ya gafarta masa, ya karɓe shi a Aljanna Firdaus, tare da jajantawa iyalan marigayin da daukacin ’yan Najeriya.
Asali: Legit.ng


