Jami'an EFCC Sun Kai Samame Otel din Obasanjo, an Samu Bayanai

Jami'an EFCC Sun Kai Samame Otel din Obasanjo, an Samu Bayanai

  • Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) sun tarwatsa wani bikin shagali da wasu matasa suka shirya a jihar Ogun
  • Sun dai kai samame ne a otel din tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda suka cafke wasu matasa da ake zargin 'yan damfarar yanar gizo ne
  • Mahukantan wurin sun tabbatar da aukuwar lamarin amma ba su bayar da cikakkjn bayanai ba kan abin da ya auku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ogun - Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun kai samame a dakin karatu na shugaban lasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a jihar Ogun.

Jami'an na hukumar EFCC sun cafke wasu matasa da ake zargin ‘yan damfara ne ta hanyar yanar gizo (Yahoo).

Jami'an EFCC sun kai samame a Ogun
Jami'an EFCC sun dura a otel din Obasanjo Hoto:@OfficialEFCC
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta gano cewa jami’an EFCC sun gudanar da samamen ne da safiyar Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a sallar isha, sun kashe wasu da dama

Jami'an EFCC sun dura kan 'yan Yahoo

Jami'an na EFCC sun kai samamen ne a lokacin wani taro da aka yi da daddare a sashen otel din OOPL, mallakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda wasu matasa suka rika gudu suna neman tsira yayin samamen.

Rahotanni sun ce jami’an sun cafke matasa da dama tare da kwace motoci masu tsada sama da guda 20 da wasu kayayyaki masu daraja.

Wani jami’in EFCC ya bayyana cewa jami’an daga sashen hukumar na Legas ne suka gudanar da aikin, rahoton The Punch ya tabbatar.

Shugaban kamfanin OOPL Ventures, Mista Vitalis Ortese, ya tabbatar da faruwar lamarin.

"Mun samu wannan bayanin kuma muna bincike kan abin da ya faru a hakika. Don haka muna kokarin jin daga wurinsu (EFCC) abin da ya faru.”
"Ina rokon ku fahimce ni, ban da karin bayani yanzu. Da zarar mun samu cikakken bayani zan sanar da ku."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga a Bauchi, an kashe miyagu

- Vitalis Ortese

Da aka tambaye shi ko jami’an EFCC ne suka zo, sai ya ce:

"Eh, su ne. An samu aukuwar wani lamari da safe. Za mu bincika kuma za mu sanar da ku.”

Lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya yi alkawarin tabbatar da batun sannan ya dawo da amsa.

Jami'an EFCC sun kai samame a otel din Obasanjo
Jami'an EFCC sun cafke 'yan Yahoo a Ogun Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan hukumar EFCC

Shugaban EFCC ya kare kansa kan Bayo Ojulari

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar EFCC ya yi martani kan zargin cewa ya tilastawa Bayo Ojulari yin murabus daga shugabancin kamfanin NNPCL.

Ola Olukoyede ya musanta cewa da hannunsa a cikin zargin sacewa tare da tilastawa shugaban na kamfanin NNPCL yin murabus daga mukaminsa.

Shugaban na EFCC ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan masu yada labaran idan ba su fito sun nemi afuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng