Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari 'Gidansu Atiku,' Sun Yi Garkuwa da Mata
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Gidansu Atiku a Malumfashi, suka yi garkuwa da mata biyu da sace shanu
- Matasan kauyukan Dan Bawa da Yan Doka sun fatattaki ‘yan bindigar, suka kubutar da matan da aka sace tare da kwako dabbobin
- A garuruwan Kurfi da Dutsinma, ‘yan bindiga sun kashe mutane, sun yi garkuwa da wasu, tare da sace shanu, tumaki da awaki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gungun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari karamar hukumar Malumfashi da ke Kudancin jihar Katsina.
Majiyoyi sun shaida cewa 'yan bindigar sun farmaki kauyen 'Gidansu Atiku' da ke cikin karamar hukumar, da yammacin ranar Asabar.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hari Gidansu Atiku
Mai kawo rahoton kan ayyukan tsaro daga Katsina, @Bakatsine ya wallafa a shafinsa na X a ranar 9 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Bakatsine ya nuna cewa 'yan ta'addar sun yi garkuwa da mata biyu tare da sace shanu biyu a harin da suka kai Gidansu Atiku.
Sai dai an rahoto cewa 'yan bindigar ba su yi nasarar tserewa da wadanda suka sace ba domin sun gamu da fusatattun matasa daga kauyukan Dan Bawa da Yan Doka.
An ce al'ummar wadannan garuruwa biyu sun yi kukan kura sun afkawa 'yan ta'addar, inda suka samu nasarar kwace mutane da dabbobin da aka sace.
Harin 'yan bindiga a garin Kurfi
Wannan na zuwa ne yayin da Bakatsine ya rahoto cewa 'yan bindiga sun kai mummunan hari garin Lambo da ke karamar hukumar Kurfi, a jihar Katsina.
Rahoton ya nuna cewa 'yan ta'addar sun kashe mutum daya, sun kuma yi garkuwa da mutane masu yawa ciki har da mata da kananan yara.
An rahoto cewa 'yan ta'addar ba su tsaya kan mutane kadai ba, domin sun yi awon gaba da shanu, tumaki da awakai masu yawa a harin da suka kai ranar Asabar.

Source: Original
'Yan bindiga sun farmaki garin Dutsinma
A hannu daya kuma, 'yan ta'dda sun mamaye garin Unguwar Bera da ke cikin gundumar Makera a karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.
A yayin wannan harin da suka kai ranar Juma'a, 8 ga watan Agusta, 2025, 'yan ta'addar sun kashe wani mutumi mai suna Ibrahim Dummai.
An kuma ce a yammacin Asabar 'yan ta'addar sun kuma sake kai hari Dutsinma, inda suka harbi mutane biyu a kusa da titin Tashar Mangoro-Dogon Ruwa, inda aka garzaya da su asibitin Katsina da Dutsinma.
Legit Hausa ta tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu game da wadannan hare-haren da aka kai.
Abubakar Sadiq Aliyu ya ce zai tuntubi Legit da karin bayani idan ya samu cikakken bayanai game da hare-haren, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton ba a ji daga gare shi ba.
Sokoto: 'Yan ta'adda sun farmaki masu ibada
A wani labarin, mun ruwaito cewa, miyagun 'yan bindiga sun farmaki masu ibada a garin Marnona da ke karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto.
An ce 'yan ta'addar sun farmaki mutanen ne a daren ranar Asabar, 9 ga Agusta, 2025 a lokacin da suke tsakiyar sallar Isha'i.
Rahoton da aka samu ya nuna cewa miyagun sun yi harbi kan uwa da wabi, inda suka samu wasu tare da yin garkuwa da wasu da dama zuwa daji,
Asali: Legit.ng


