"Ta Fi Ta Sau 100": Amaechi Ya Kwantanta Gwamnatin Buhari da Ta Shugaba Tinubu
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan yadda rayuwa take a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta Shugaba Bola Tinubu
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta fi ta Shugaba Tinubu nesa ba kusa ba wajen yin rayuwa mai kyau
- Tsohon ministan ya nuna cewa yanzu rayuwa ta yi tsada fiye da yadda abubuwa suke a lokacin da marigayi Buhari yake kan madafun ikon kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta fi ta Shugaba Bola Tinubu.
A cewarsa, gwamnatin Buhari ta fi ta Tinubu “sau 100”, yana mai danganta hakan da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.

Asali: Twitter
Amaechi ya yi wannan furuci ne wata tattaunawa da aka yi a X Spaces mai taken “Weekend Politics”, wadda jaridar Tribune ta bibiya a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
Kungiyoyin Arewa sama da 1,000 sun tsaida wanda za su zaɓa tsakanin Tinubu da Atiku a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Amaechi ya ce kan gwamnatin Buhari da Tinubu?
Ya bayyana cewa a lokacin gwamnatin Buhari, ba a mutuwa saboda yunwa.
"Gwamnatin Buhari ta fi ta Tinubu sau 100. Don Allah, a lokacin kuna mutuwa da yunwa ne? Yanzu muna biyan N1,000,000 a kowane mako don wutar lantarki (N4,000,000 a wata)."
"Ta Yaya mutane za su iya biyan haka? Sannan sai ka kara sayen dizal da kusan N300,000, banda ciyarwa da albashin ma’aikata."
- Rotimi Amaechi
Ya kara da cewa halin da ake ciki yanzu ya fi muni, inda ya yi ikirarin cewa a lokacin mulkin Buhari, rayuwar ‘yan Najeriya ta fi ta yanzu inganci.
“Bai kasance haka ba lokacin da Buhari ke kan karagar mulki. Me yasa za mu kwatanta lu’ulu’u da zinariya? A gaskiya ma, wannan gwamnati ba ma zinariya bace."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya shiga hadaka
Kwatancen Amaechi ya biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa ADC, inda yanzu yake tare da wasu fitattun mutane kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan
Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock
Wannan sabon kawancen na da nufin kifar da Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC a zaben 2027.
Amaechi ya kuma yi alkawarin goyon bayan duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC muddin aka gudanar da sahihin zaben fidda gwani.

Asali: Facebook
Karanta wasu labaran kan Rotimi Amaechi
- Amaechi: Tsohon ministan Buhari ya kalubalanci 'yan siyasar Najeriya
- ADC: Amaechi ya kada hantar Tinubu kan zaben 2027, ya fadi illar da zai yi masa
- Amaechi: Matsala ta tunkaro Tinubu bayan tsohon minista ya sha alwashi a kansa
Amaechi sha alwashi kan cin hanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimii Amaechi, ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa idan ya zama shugaban kasa.
Amaechi ya bayyana cewa zai batar da cin hanci da rashawa idan ya zama shugaban kasa a cikin wata daya kacal.
Ya sha alwashin cewa idan ya gaza cimma hakan zai rubuta takaradar murabus domin ya sauka daga kan mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng