Ta Fara Tsami: Shehi Ya Gorantawa Murtala Asada game da Tattaunawa da Bello Turji
- Sheikh Adam Muhammad Albaniy ya goyi bayan tattaunawa da Bello Turji, yana yaba wa kokarin Malam Musa Assadus Sunnah wajen rage kashe-kashe
- Sheikh Albaniy ya caccaki Malam Murtala Bello Asada, yana tambayarsa irin gudunmawar da ya bayar ga al’ummar Zamfara da Sokoto wajen magance matsalar tsaro
- Ya bayyana takaicinsa kan malamai masu sukar wasu amma ba sa bayar da taimako, yana kalubalantar Asada da ya tafi tare da shi zuwa wurin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Maganar tattaunawa da Bello Turji ya yi da malamin Musulunci ya fara zafi a Arewacin Najeriya tsakanin malamai.
Wasu daga cikinsu suna sukar lamarin yayin da Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya yaba da lamarin.

Source: Facebook
Turji: Sheikh Albaniy ya soki Malam Asada
Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook.
A cikin bidiyon, Malam Albaniy ya soki Sheikh Murtala Bello Asada kan sukar tattaunawa da aka yi ko ake yi da Bello Turji a Zamfara.
Sheikh Albaniy ya dauki zafi inda ya kalubalanci Malam Asada kan maganganunsa game da lamarin.
Shehin malamin ya yabawa Musa Assadus Sunnah kan kokarin kubutar da al'ummar game da halin da suke ciki.
Ya ce:
''Malam wanene, Murtala Asada, Malam Musa yana iya bakin kokarinsa, kuma muna tare da shi duniya ta sani.
"Muna tare da shi a kan wannan yunkuri na sassauta yadda ake kashe bayin Allah.
"Idan har muka koma ga Allah ba mu kawo karshen wannan matsalar ba muna ladan kokari ko ba mu da shi?, muna da lada."

Source: Facebook
Kalubalen da Albaniy ya tura ga Malam Asada
Sheikh Albaniy ya caccaki Asada inda ya kalubalancr shi kan ya bayyana gudunmawa da ba al'umma a wannan ɓangare a yankinsa.
Ya bayyana takaici yadda wasu ba za su ba da gudunmawa su sadaukar da rayuwarsu ba kan al'umma amma suna sukar wasu.
Ya kara da cewa:
"Kai da kake da kororoto an yi kaza an yi kaza, kai da kake yankin Zamfara da Sokoto wacce gudunmawa ka ba al'umma don kubutar da rayuwarsu.
"A matsayinka na malami mai da'awa da ke tsakanin Zamfara da Sokoto wanda bai da gwamnati a hannunsa wacce gudunmawa ka ba al'ummar yankin, Muna neman ka da wannan jawabi.
"Shi malam Musa ya yi nasa tare da taimakon wasu malamai yana kubutar da wasu.
"Mutane babu abin da kuke yiwa al'umma wurin kawo mata sauki sai wadanda suka sadaukar da rayuwarsu, wallahi da dani za a je, wani aiki ne daban ya hana ni, Idan kai jarumi ne na gaske ka zo mu je tare da kai."
Sheikh Albaniy ya soki tsohon Minista
Mun ba ku labarin cewa ana zargin cewa Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya soki tsohon minista, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a jihar Gombe.
Albaniy ya nuna Pantami bai tallafawa limamai ko ladanai ba lokacin da yake minista, yana mai zargin rashin taimako ga addini.
Masoyan Pantami sun kare shi, suna cewa ya gina masallaci a makarantar sakandare a birnin Gombe.
Asali: Legit.ng


