Bidiyo: Abin da Amarya Rahama Sadau Ta Yi bayan Ɗaura Aurenta Ya Ja Hankali
- Ƴan uwa da abokan arziki sun zagaye Rahama Sadau suna taya murna bayan ɗaura aurenta yau Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025 a Kaduna
- A wani faifan bidiyo da aka fara yaɗawa, an ga Rahama Sadau zaune a ɗaki yayin da kawaye da ƙannenta suka rika faɗin "an ɗaura an ɗaura"
- Ɗan uwan jarumar, Abba Sadau ya bayyana cewa Rahama ta yi aure ne domin cika burin mahaifinsu, wanda Allah ya yiwa rasuwa kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - A yau Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025 aka samu labarin cewa fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau ta shiga daga ciki.
Bayanai daga ƴan uwanta da abokanan arziki sun tabbatar da cewa an ɗaura auren Rahama da angonta mai suna Ibrahim Garba a masallacin unguwar Rimi, Kaduna.

Asali: Instagram
Ɗan uwan jarumar, Abba Sadau ya tabbatar da haka ga wakilin DCL Hausa a wata hira da aka yi da shi bayan ɗaura auren yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni dai ƴan uwa da abokanan arziki suka fara tura saƙonnin murna da fatan alheri ga Rahama Sadau, wacce ta shiga sabuwar rayuwa ta ibada a musulunci.
Rahama Sadau ta cika burin mahaifinta
Sai dai Abba Sadau ya bayyana cewa mahaifinsu ya so ya ga auren ƴaƴansa tun yana raye, amma Allah bai tsara hakan ba.
A cewarsa, wannan dalili ya sa tun bayan rasuwar mahaifinsu, Rahama Sadau ta yi alƙawarin cewa ba da jimawa za ta yi aure don cika burin babansu.
Sai dai jim kaɗan bayan ɗaura auren, shafin Arewa family weddings na Istagram ya wallafa bidiyon amarya zaune a ɗaki ana zuwa ana taya ta murna.
Bidiyon Amarya Rahama Sadau ya fara yawo
A faifan bidiyon, an ga Rahama Sadau zaune yayin da kawayenta da ƙannenta ke shigowa suna rangaɗa buɗa tare da taya ta murna, suna faɗin, "an ɗaura an ɗaura,"

Kara karanta wannan
A ƙarshe, Rahama Sadau ta fitar da saƙo ga masoya bayan ɗaura aurenta a masallaci
Ɗaya daga cikin matan da aka ji muryoyinsu a bidiyon ta buƙaci Amarya ta yi murmushi ganin yadda ta zauna ko shiryawa ba ta yi ba, kuma babu wata fara'a a fuskarta.
"Murmushi ya kamata ki yi ranar farin ciki ce, shi ne jin daɗin rayuwa," in ji wata a cikin bidiyon, yayin da wata kuma ta zolaye ta da cewa "kamar auren dole."
Shafin ya rubuta saƙon murna a jikin bidiyon da cewa:
"Alhamdulillah, an ɗaura an ɗaura, Rahama Sadau kin zama kin zama ɗauko riga, kin zama ɗauko hula, Allah ya yiwa aurenki Albarka, Allah Ya baku zaman lafiya."
Jaruma Rahama Sadau ta shiga daga ciki
A baya, kun ji cewa an ɗaura auren Jaruma Rahama Sadau ba tare da sanarwa ba a masallacin Unguwar Rimi da ke jihar Kaduna.
Abba Sadau, ɗan uwan jarumar ya bayyana cewa ba kowa ya san da ɗaura auren ba har sai da aka ɗaura yau Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025.
Masoyan jarumar daga fannoni daban-daban sun yi mata addu’o’i na samun zaman lafiya, hakuri, da dorewar soyayya a tsakaninta da angonta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng