Jami'an Tsaro Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Bauchi, an Kashe Miyagu

Jami'an Tsaro Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Bauchi, an Kashe Miyagu

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar mugun iri bayan sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • A yayin fafatawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu, an samu nasarar tura 'yan bindiga guda biyu zuwa lahira
  • Hakazalika, jami'an tsaron sun fatattaki ragowar 'yan bindigan zuwa cikin daji tare da kwato wasu daga cikin makaman da suke amfani da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - An samu nasarar kashe 'yan bindiga yayin wani gagarumin aikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da aka gudanar a jihar Bauchi.

Jami'an tsaron sun kashe 'yan bindiga guda biyu tare da kwato bindigar AK-47 daga hannunsu a karamar hukumar Alkaleri.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Bauchi
Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga yayin artabu a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga

Lamarin dai ya auku ne a ranar Juma'a, 8 ga Agusta, 2025 bayan an gwabza fada tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, jami'an tsaro da suka hada da 'yan sa-kai sun hango wasu ’yan bindiga guda shida a tsakanin ƙauyen Dogon Ruwa da dajin Yakaki.

Jami'an tsaron sun hango 'yan bindigan ne dai dauke da makamai yayin wani aikin sintiri na yau da kullum.

Bayan ganin waɗanda ake zargi, tawagar jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai sun bi sawunsu a hankali, inda suka shirya musu kwanton ɓauna.

Wannan mataki ya haifar da musayar wuta mai tsanani amma ta ɗan gajeren lokaci.

A yayin wannan arangama, an kashe ’yan bindiga biyu a wurin, yayin da sauran huɗun suka tsere cikin dajin da ke kusa.

Haka kuma, jami’an tsaro sun kwato bindigar AK-47 ɗaya wadda ba ta da harsasai daga hannun waɗanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Masu sayar wa ƴan ta'adda bindigogi sun gama guje guje, sun shiga hannu a Kaduna

Bayanan da suka fito daga jami’an tsaro sun nuna cewa wannan aikin ya kasance sakamakon ƙarin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’ummar yankin.

Lamarin ya kara fito da irin muhimmiyar rawar kungiyoyin sa-kai ke takawa wajen taimaka wa gwamnati kan yaki da ta’addanci da satar mutane a yankunan karkara.

'Yan bindiga sun yi artabu da jami'an tsaro a Bauchi
Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Bauchi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun sace matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun tare matafiya suna tsaka da tafiya kan wata hanya a jihar Kogi.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da wasu daga cikin fasinjojin motar bayan sun bude musu wuta.

Sai dai, direban motar da wasu daga cikin 'yan bindigan sun samu nasarar tsira daga kamun 'yan bindigan bayan sun gudu zuwa cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel