'Yan Bindiga Sun Tare Matafiya a Hanya, an Yi Awon Gaba da Fasinjoji
- Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun tare matafiya yayin da suke tsaka da tafiya kan hanya a jihar Kogi
- Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da wasu daga cikin fasinjojin da lamarin ya ritsa da su bayan sun yi musu kwanton bauna
- A wani abin mamaki, direba da wasu fasinjoji sun samu nasarar tserewa fadawa hannun miyagun 'yan bindigan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Wasu ’yan bindiga sun sace fasinjoji tara a wurin da ake kira kwanar Ogbabo a kan hanyar Itobe–Anyigba a jihar Kogi.
A yayin harin, direba da wasu fasinjoji shida sun kubuta daga kamun ba zato ba tsammani.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a ranar Juma’a, 8 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Kogi

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka
Lamarin ya auku ne a kusa da kwanar Ogbabo, cikin karamar hukumar Ofu, inda aka tarar da wata bas mai lambar rajista ENZ-55 XS da wata mota kirar Toyota Carina “E” mai launin shuɗi a ajiye.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigan, waɗanda suka yi kwanton ɓauna a wajen, sun fito kwatsam a kan babban titin lokacin da suka hango wata babbar mota kirar Hummer cike da fasinjoji na tahowa.
’Yan bindigan sun tilasta wa motar tsayawa tare da yin harbi don tsoratar da fasinjojin, waɗanda ke tafiya a cikin wata mota da ake tunanin suna kan hanyarsu zuwa yankin Gabashin ƙasar nan ne.
Sai dai direban motar, wanda aka bayyana sunansa da Mista Sunday Okechi, ya yi dabara ya kauce musu, ya tsere cikin daji tare da wasu fasinjoji shida.
Amma sauran fasinjoji tara ba su yi sa’a ba, domin ’yan bindigan sun tilasta musu shiga cikin dajin da ke kusa.
Wurin da aka yi satar bai wuce mita 300 daga wani shingen duba ababen hawa na sojoji a kan hanyar Ogbabo–Ochadamu ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Jami’an tsaro sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da motar bas ɗin mai lambar ENZ-55 XS da kuma motar Toyota Carina “E” a ajiye, kuma an tura su zuwa wurin ajiya mai aminci.
Hukumomin tsaro tare da haɗin gwiwar ƙungiyar 'yan sa-kai da mafarauta sun fara bincike da aikin ceto don gano inda ’yan bindigan suke da kuma kubutar da waɗanda aka sace.

Source: Original
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Hukumar ’yan sandan jihar Kogi ba ta bayar da wani bayani kan lamarin ba tukuna har zuwa lokacin da muke tattara wannan labari.
Haka zalika ba a iya samun kakakin hukumar, SP Williams Ovye, a waya ba, domin layinsa yana kashe da safiyar yau.
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Birnin Magaji, inda suka yi awon gaba da mutane hudu.
Ana zargin 'yan bindigan sun kai harin ne saboda wani jami'in 'yan sa-kai da yake taimakawa jami'an tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
