Daga Zuwa Aiki a Najeriya, Ɗan Ƙasar China Ya Yi Mutuwar da ba a Saba Gani ba

Daga Zuwa Aiki a Najeriya, Ɗan Ƙasar China Ya Yi Mutuwar da ba a Saba Gani ba

  • An tabbatar da mutuwar ɗan kasar China, Luo Zhi Mao, mai shekara 47 da haihuwa bayan ya faɗi a wani kamfani a jihar Kogi
  • Rahotanni sun nuna cewa an yi ƙoƙarin ceton rayuwar ɗan ƙasar wajen, amma ya cika bayan kwanaki huɗu da faruwar lamarin
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa tuni jami'anta suka fara binciken gano sanadin mutuwarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wani ɗan ƙasar China mai shekaru 47 da haihuwa, mai suna Mista Luo Zhi Mao, ya faɗi ya rasu a kamfanin BN Ceramics da ke Ajaokuta, Jihar Kogi.

Ɗan kasar wajen, wanda aka ce shi ne mai duba ayyuka a kamfanin, ya gamu da ajalinsa ne a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun fara binciken kisan 'ɗan fashi' bayan koken uwarsa

Dan China ya rasa ransa a kamfani a Kogi.
Dan ƙasar China ya mutu a wani kamfani a jihar Kogi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa bayan ya yanke jiki ya faɗi, an garzaya da shi asibitin da ke Ajaokuta, daga nan aka tura shi zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya (FMC) a Lokoja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto shi, an tabbatar da rasuwar Zhi Mao a wani asibiti daban a ranar Talata da misalin ƙarfe 9:30 na dare.

Ɗan China ya yi mutuwar ba-zata a Kogi

Wani ma’aikacin kamfanin mai suna Yunusa, wanda bai so a bayyana cikakken sunansa ba, ya ce:

“An garzaya da shi zuwa Asibitin Covenant da ke Ajaokuta, inda daga nan aka tura shi zuwa Asibitin Koyarwa, tsohuwar FMC da ke Lokoja, saboda yanayin da yake ciki ya tsananta.
“Babu ma’aikatan da za su kula da shi yadda ya kamata a asibitin saboda yajin aikin da ke gudana a lokacin; Sai aka ɗauke shi zuwa Asibitin Kudi na Shifaah da ke Lokoja. A nan ya mutu bayan kwana huɗu.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sandan Kano ta fara binciken kisan hadimin gwamna, sadiq Gentle

Duk wani ƙoƙarin jin ta bakin hukumar gudanarwar kamfanin game da lamarin bai yi nasara ba, domin wani ma’aikaci ya ce da wahala su yi magana har sai an gama binciken gawa.

Ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar, SP William Aya, ya ce ɗan ƙasar China ya rasu ne sakamakon abin da ake zargin yana da alaƙa da rashin lafiya.

Jami'an yan sandan Najeriya.
Rundunar yan sanda ta fara bincike kan mutuwan ɗan China a Kogi Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano ainihin dalilin mutuwarsa, kuma za a mika sakamakon ga hukumomin da suka dace idan an kammala.

A halin yanzu, an ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararru na Jihar Kogi domin gudanar da bincike.

Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a Borno

A wani labarin, kun ji cewa an tsinci gawarwakin iyalan mutum huɗu a cikin gidansu a yankin ƙaramar hukumar Hawul ta jihar Borno.

Wadanda suka rasu sun hada da magidanci, Yakubu Samanja, matarsa mai suna Esther Yakubu, da kuma ‘ya’yansu guda biyu.

Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja shi ya fara tabbatar da faruwar lamarin bayan ya kai ziyara a gidan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262